Idin karamar sallah: Masarautar Kano za ta yi hawan daba
- Masarautar Kano ta sanar da cewa zata yi hawan sallah daga cikin shagalin bikin karamar Sallah mai zuwa
- A wata wasika da ta aika ga dukkan hakimanta, ta bukacesu tare da dagatai da fadawansu da su hallara a Kano a ranar Litinin
- Wannan ne karon farko da za a yi hawan sallah a birnin Dabo tun bayan hawan sarki Alhaji Aminu Ado Bayero
Masarautar Kano ta ce za ta yi hawan gargajiya na sallah da ta sa saba yi domin shagalin bikin murnar karamar sallah a jihar.
Wannan ne zai zama hawan daba na farko da za a yi a jihar tun bayan hawan Alhaji Aminu Ado Bayero karagar mulkin Kano.
Idan za mu tuna, a 2020, gwamnatin jihar ta dakatar da yin hawan sallah saboda annobar korona da ta zagaye duniya.
KU KARANTA: Da duminsa: An sheke jami'an 'yan sanda 6 yayin da 'yan bindiga suka kai farmaki ofishin 'yan sanda
KU KARANTA: Kano: Barkewar amai da gudawa ta janyo rasa rayuka 15, 40 suna asibiti kwance
A wasikar da masarautar ta tura ga dukkan hakimanta kuma Daily Trust ta gani, ta bada umarnin su fara tattaruwa a fadar sarkin a ranar Litinin domin shirye-shiryen hawan.
"An umarceku da ku shiga Kano tare da dukkan dagatanku, dogarai da dawakinku a ranar Litinin, 28 ga watan Ramadan, 1442 wanda yayi daidai da ranar 10 ga watan Mayun 2021 domin fara shirin shagalin idin shekarar nan," wani bangaren wasikar ya sanar.
Wasikar wacce Awaisu Abbas Sanusi yasa hannu a madadin sakataren masarautar, ta bukaci dukkan masu sarautar gargajiya da su hadu a fadar sarkin a ranar Talata domin taro.
Wannan hukuncin na masarautar yana zuwa ne bayan masarautun Bauchi, Neja da na Daura ta jihar Katsina sun dakatar da shagalin bikin sallah saboda rashin tsaro.
Amma dai jihar Kano za a iya cewa akwai zaman lafiya duk da matsalolin tsaron da suka addabi Katsina da Kaduna masu makwabtaka da ita.
A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da haramta kai masa gaisuwar sallah daga shugabannin addinai, yankuna da na siyasa kuma yace a fadarsa ta Aso Rock zai yi sallar Idi.
A wata takarda da shugaban kasa ya fitar ta hannun mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu, ya hori shugabanni da su zauna gidajensu don yin bikin sallah sakamakon annobar korona.
Kamar yadda takardar ta bayyana, "Yayin da Musulmin Najeriya da sauran na duniya suke hango bikin sallah, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin karanta shagulgula saboda cutar korona da ta addabi duniya "
Asali: Legit.ng