Hankula sun tashi a Onitsha bayan babbar mota dauke da harsasai ta fadi a titi

Hankula sun tashi a Onitsha bayan babbar mota dauke da harsasai ta fadi a titi

- Hankula sun daga bayan wata mota dankare da harsasai ta fadi a kan babban titin Awka na jihar Anambra

- Tuni dai direban ya sauka tare da kokarin tattare harsasan amma lamarin ya ci tura har sai da jami'an tsaro suka bayyana

- Wannan lamarin na zuwa ne bayan tsanantar rashin tsaro a yankin kudu maso gabas na kasar nan

Hankula sun tashi a garin Onitsha a ranar Lahadi bayan wata babbar mota dankare da harsasai ta fadi a kan babban titin Awka dake jihar Anambra.

Lamarin ya faru ne a sa'o'in farko na ranar Lahadi. Harsasan sun zube a yankin yayin da direban motar ya dinga kokarin kwashesu amma hakan ya gagara.

Amma kuma mazauna yankin da suke kan hanyar zuwa coci sun zo wurin sai dai tuni jami'an tsaro suka gaggauta isa titin, jaridar The Cable ta ruwaito.

KU KARANTA: Kano: Rikicin cikin gida ya kunno kai a kungiyar Kwankwasiyya

Hankula sun tashi a Onitsha bayan babbar mota dauke da harsasai ta fadi a titi
Hankula sun tashi a Onitsha bayan babbar mota dauke da harsasai ta fadi a titi. Hoto daga @TheCableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: An sheke jami'an 'yan sanda 6 yayin da 'yan bindiga suka kai farmaki ofishin 'yan sanda

Duk da babu wanda ya rasa ransa, bayan kankanin lokaci ababen hawa suka fara kaiwa da kawowa a titin yayin da jami'an tsaro suka hana mazauna yankin zuwa kusa da harsasan dake zube.

Wannan cigaban ya faru ne a lokacin da ake tsaka da rashin tsaro a jihohin yankin Kudu maso gabas.

Tuni dai miyagun 'yan daba suke kai farmaki ofisoshin 'yan sanda dake yankin kudu maso gaba, hakan ya dinga kawo rasa rayukan 'yan sanda da kone ofisoshinsu.

A wani labari na daban, a kalla mutum 15 ne suka rasa rayukansu a kauyen Koya dake karamar hukumar Minjibir ta jihar Kano bayan zargin barkewar cutar amai da gudawa a yankin.

Dagacin kauyen, Sulaiman Muhammad, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai inda yace annobar ta fi shafar mata da kananan yara.

Mazauna kauyen da suka zanta da manema labarai sun ce wadanda cutar ta shafa suna ta kwarara amai da gudawa.

Jami'an lafiya da suka isa kauyen bayan aukuwar lamarin sun hori mazauna kauyen da su guji shan ruwa daga tafkuna da rijiyoyin kauyen.

An tattaro cewa jami'ai sun kai jakkuna ruwan leda 300 kauyen a ranakun karshen mako domin takaita cigaban yaduwar muguwar annobar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: