Da Ɗuminsa: Gobara Ta Ƙone Babbar Cocin RCCG a Jihar Lagos

Da Ɗuminsa: Gobara Ta Ƙone Babbar Cocin RCCG a Jihar Lagos

- Wata gobara da ta ɓarke da sanyin safiyar ranar Lahadi a hedkwatar cocin mabiya addinin kirista na RCCG dake Alapere jihar Lagos ta laƙume kayayyakin cikin cocin da suka kai na miliyoyi

- Kakakin hukumar yan sandan jihar ya tabbatar da faruwar lamarin amma yace har yanzun ba'a gano musabbabin tashin wutar ba

- Kwamishinan yan sanda na jihar ya umarci jami'an dake yankin su baiwa ƙonanniyar cocin tsaro sabida gujewa ɓarayi daka iya zuwa suyi sata

Rahotanni daga jihar Lagos sun nuna cewa wata Gobara ta laƙume hedkwatar cocin mabiya addinin kirista (RCCG) dake Alapere da sanyin safiyar ranar Lahadi, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Jami'an Soji Sun Damƙe Mayaƙan Boko Haram 10 a Jihar Kano

Ana hasashen wutar ta ƙone kayayyakin da suka kai darajar miliyoyin nairori a cocin dake Layi mai lamba 28, Alapere jihar Lagos.

Sai-dai har yazuwa yanzun ba'a gano musabbabin gobarar ba wacce ta fara ci tun karfe 5:00 na safiyar ranar Lahadi.

Da Ɗuminsa: Gobara Ta Ƙone Babbar Cocin RCCG a Jihar Lagos
Da Ɗuminsa: Gobara Ta Ƙone Babbar Cocin RCCG a Jihar Lagos Hoto: m.guardian.ng
Asali: UGC

Mai magana da yawun hukumar yan sandan jihar Lagos, Muyiwa Adejobi, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Yace yayin da DPO na ofishin yan sandan Oguru ya samu rahoton ɓarkewar wutar, yayi gaggawar sanar da jami'an hukumar kashe wuta na jihar.

KARANTA ANAN: Wasu Yan Bindiga Sun Ƙone Ofishin Jami’an Tsaro da Motarsu, Sun Hallaka Mutum Biyar

Mai magana da yawun yan sandan yace:

"An samu nasarar kashe wutar, kuma babu wani da ya rasa ransa sanadiyyar lamarin, Kayayyakin dake cikin cocin ne kaɗai suka salwanta."

"Har yanzun bamu san musabbabin ɓarkewar wannan wutar ba. Kwamishinan yan sanda na jihar Lagos, Hakeem Odumosu, ya umarci DPO na yankin da ya baiwa wurin tsaro yadda yakamata domin gujewa sace wasu abubuwa a wajen."

"Hukumar kashe wuta ta jihar Lagos zata fara bincike kan lamarin domin gano abinda ya jawo wannan mummunar gobara."

A wani labarin kuma Wasu Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 11 a Sabon Hari Da Suka Kai Jihar Katsina

Wasu yan bindiga sun kai hari a garin Tsatskiya dake ƙaramar hukumar Safana, jihar Katsina inda suka hallaka mutum 11 tare da jikkata wasu da dama.

Maharan sun isa garin ne da misalin ƙarfe 9:30 na safiyar Ranar Asabar domin ɗaukar fansa a kan kisan da mutanen garin suka yi wa ɗan leƙen asirinsu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel