Kano: Rikicin cikin gida ya kunno kai a kungiyar Kwankwasiyya
- Rikicin cikin gida ya kaure a Kwankwasiyya ta jihar Kano bayan an zargi wani mabiyin tafiyar da yunkurin son fitowa takarar gwamna
- Kamar yadda hadimin Kwankwaso, Sanusi Surajo yayi magana, ya ce Abba Gida Gida ya samu karbuwa kuma shi zai sake fitowa, ba zasu karba kowa ba
- Tsohon Kwamishina kuma shugaban ma'aikatan fadar Kwankwaso yayin mulkinsa, Dangwani, shine ya raba kayan azumi, lamarin da yasa ya fara tara magoya baya
Hargitsin cikin gida ya fara tsakanin mabiyan kungiyar Kwankwasiyya dake jihar Kano. Hakan ta faru ne sakamakon rabon kayan abinci na azumi na miliyoyin naira da wani yayi wa 'yan jam'iyyar a Kano.
Hadimin sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Sanusi Surajo, ya sanar da cewa ya ga wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta inda Dakta Adamu Dangwani ke shirin farraka kan 'yan Kwankwasiyyan.
Dangwani tsohon kwamishinan ruwa ne kuma shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin Kano yayin mulkin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
A zargin da ake masa, akwai na kalubalantar Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida Gida saboda bai samu damar takara ba a 2019.
KU KARANTA: Gara mu rasa rayukanmu da a tsige Buhari daga kujerarsa, Masoyan shugaban kasa
KU KARANTA: Sanata ya bukaci majalisa ta dauka tsatsauran mataki a kan mulkin Buhari
Kamar yadda Sanusi Surajo ya sanar, "Babu dan takarar gwamnan da za mu yi na'am da shi ban da Abba Gida Gida, hakan yasa zamu yi watsi da duk wani kira na daban, don haka Dangwani yayi watsi da kudirinsa ko kuma ya bar tafiyarmu.
"Hatta Kwankwaso ba zai sauya mana Abba ba, idan baka bayan Abba, toh abu mafi sauki shine ka fice da tsarin ko ka bar jam'iyyar baki daya.
"Abba ya samu karbuwa kuma ba za mu canza shi ba. Muna sane da irin zagon kasa da ake yi wa Sanata Kwankwaso kuma ba wanda zai ci galaba da izinin Allah."
Dangwani ya fara suna ne bayan rabon kayan azumi da yayi ga 'yan Kwankwasiyya. Yanzu haka dai yana samun magoya baya daga shugabanni da mambobin Kwankwasiyya kuma suna kira garesa da ya fito takarar Gwamnan jihar.
Har a halin yanzu, ba a ji uffan daga bangaren Dangwani ba kan zargin da ake masa.
A wani labari na daban, duk da shigar 'yan sanda tashin hankalin dake faruwa a yankin Mile 12 a jihar Legas, kungiyoyin dake fada sun cigaba da tada zaune tsaye.
Premium Times ta ruwaito yadda 'yan sanda suka cafke mutum 45 da ake zargi bayan rikicin ya barke a yankin Mile 12.
'Yan sandan sun ce lamarin ya faru ne bayan zargin wani Alhaji Alidu da aka yi da batanci ga Annabi Muhammad. Shine kwamandan kungiyar 'yan sintirin yankin Gengere.
Asali: Legit.ng