Da duminsa: Da yiwuwan rokan China da ya bace a sararin samaniya ya fadi a Abuja

Da duminsa: Da yiwuwan rokan China da ya bace a sararin samaniya ya fadi a Abuja

- Wani Rokan da kasar Sin ta harba sararin samaniya na shirin fadowa duniya wannan makon

- Masana sun bayyana cewa ba'a san takamammen inda wannan roka zai fadi ba

- An lissafa Abuja cikin jerin biranen da roka ka iya fadowa

Wani rahoton NBC News ya nuna cewa rokan da kasar Sin ta harba sararin samaniya a Afrilun 2021 na shirin dawowa duniya yau Asabar, 8 ga Mayu, ko Lahadi 9 ga Mayu, bisa hasashen masana.

A cewar Rahoton, rokan mai girman gida mai tsauni 10 na yawo a sararin samaniya yanzu hakan da gudun mil 18,000/hr.

Yayinda ba bakon abu bane sassan roka ya fado duniya, wannan ya zama abin damuwa saboda rokan ya bace ne kuma babu tabbacin inda zai fadi.

Masana Kimiya sun bayyana cewa yiwuwar idan ta fado za ta kashe mutum na da kamar wuya, amma zai yiwu.

An bayyana jerin biranen da ake ganin da yiwuwar ta fado.

Biranen sune; New York, Los Angeles, Madrid, Rio de Janeiro, Beijing, da birnin tarayyar Abuja.

Masanan sun kara da cewa an fi kyautata zaton rokan zai fadi ne cikin teku.

KU KARANTA: Ba zai yiwu a ga wata ranar Talata a Najeriya ba, amma dai a duba: Kwamitin duban wata

Da duminsa: Da yiwuwan rokan China da ya bace a sararin samaniya ya fadi a Abuja
Da duminsa: Da yiwuwan rokan China da ya bace a sararin samaniya ya fadi a Abuja
Asali: Getty Images

DUBA NAN: Zargin Badakalar N165bn: Ainihin dalilin da ya sa Buhari ya dakatad da Hadiza Bala Usman

A Disamban 2019 wata bakuwar cuta ta bulla a garin Wuhan ta Sin wacce ta hallaka dimbin mutane har da Likitan da ya ankarar da gwamnati.

Zuwa Junairu, wannan cuta ya fara yaduwa a fadin duniya kuma kungiyar lafiya ta duniya WHO ta sanyawa sunar cutar COVID-19.

Daga baya WHO tace wannan cuta ta zama annoba a duniya.

Kawo yanzu 2021, cutar COVID-19 ta kama mutum milyan 157. Yayinda mutum milyan 93.1 suka samu waraka, mutum 3.27 sun rigamu gidan gaskiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel