Da dumi-dumi: IPOB ta sha mummunan kaye yayin da Sojojin Najeriya suka kashe mayaƙan kungiyar 11

Da dumi-dumi: IPOB ta sha mummunan kaye yayin da Sojojin Najeriya suka kashe mayaƙan kungiyar 11

- Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta kashe wasu mambobin haramtaciyyar kungiyar nan ya Biafra su 11

- An kashe maharan ne a yayinda suka kaddamar da hari kan rundunar' yan sanda na karamar hukumar Orlu da ke Jihar Imo a daren Alhamis

- Hakazalika jami'an tsaron hadin gwiwa sun yi nasarar dakile harin nasu, sun kuma kwato makamai daa wajensu

Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da cewa ta kashe mambobin kungiyar Eastern Security Network (ESN) da ke da alaka da haramtacciyar kungiyar, Indigenous People of Biafra su 11.

Rundunar sojin ta bayyana cewa dakarunta sun kashe mayakan na ESN a lokacin da suka kaddamar da hari kan kwamandan ‘yan sanda na karamar hukumar Orlu na jihar Imo a daren ranar Alhamis, 6 ga watan Mayu.

Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Birgediya Janar, Mohammed Yerima, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Facebook a ranar Juma’a, 7 ga watan Mayu.

Da dumi-dumi: IPOB ta sha mummunan kaye yayin da Sojojin Najeriya suka kashe mayaƙan kungiyar 11
Da dumi-dumi: IPOB ta sha mummunan kaye yayin da Sojojin Najeriya suka kashe mayaƙan kungiyar 11
Asali: Getty Images

KU KARANTA KUMA: Matasan Najeriya 5 da suka daukaka martabar kasar a idon duniya, karamin cikinsu shekararsa 10

Sanarwar ta ce:

“Wasu gungun‘ yan ta’adda na IPOB / ESN a cikin motoci a ranar Alhamis, 6 ga watan Mayu 2021, sun afka wa garin Orlu da nufin kai hari a harabar da ke dauke da rundunan ‘Yan Sanda a karamar Hukumar Orlu ta Jihar Imo.

“Jami’an‘ yan sanda da ke yankin sun dakile harin, kuma an fatattake su gaba daya lokacin da wata tawaga ta hadin gwiwa ta Sojojin Najeriya da na Sojan Sama na Najeriya suka iso wurin.

“Maharan wadanda suka kasance tawagar Hadin gwiwar Kwararru ta Fasaha sun fito ne daga wani Sansanin Daji da ke karamar Hukumar Ideato ta Arewa ta Jihar Imo daga inda suka taru kuma suka shirya harin da bai yi nasara ba.

“Bayan arangamar, an kashe yan ta’addan IPOB / ESN goma sha daya yayin da aka samu bindigogin AK47 guda hudu, G3 guda daya da kuma bindiga kirar berretta, layu da alburusai daban-daban. Dukkanin motocin aiki guda bakwai da aka yi amfani da su don harin an lalata su kuma don haka sauran 'yan ta'addar suka tsere da kafa da munanan raunuka.

“Babu asarar rayuka a bangaren jami’an tsaro.

“An shawarci‘ yan kasa masu bin doka da oda a yankin da su nemi baƙon da ke da rauni na harbin bindiga sannan su kai rahoto ga hukumar tsaro mafi kusa don tsaron lafiyar garuruwansu.

“Sojojin Najeriya na ci gaba da jajircewa kan dunkulalliyar Najeriya wacce za ta kasance mai aminci ga dukkan yan kasa masu bin doka kuma za ta ci gaba da taimaka wa ‘yan sanda wajen tabbatar da tsaron cikin gida.

KU KARANTA KUMA: Da duminsa: Fasinjoji 14 Sun Kone Kurmus Yayin da Motar Bas Ta Kama Wuta a Kan Babbar Hanyar Legas Zuwa Ibadan

"An sake umartar jama'a da su tallafawa jami'an tsaro da bayanai masu amfani kuma cikin lokaci wadanda za su taimaka wajen kawar da barazanar tsaro a cikin al'ummominsu."

A baya mun ji cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba a daren Alhamis, 6 ga Mayu, sun yi yunkurin kai hari Hedikwatar’ Yan sanda ta Orlu a jihar Imo.

Jami'an tsaro a wani aikin hadin gwiwa, sun dakile harin kuma sun kashe akalla mutane takwas daga cikin maharan, jaridar The Punch ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel