Muna hasashen za'ayi ambaliya a jihohi 28 bana, Ministan Ruwa ya lissafo su
- Gwamnatin tarayya ta bayyana wuraren da ake sa ran fuskantar Ambaliya a shekarar 2021
- Ministan ruwa ya bayyana cewa ba'a son abinda ya faru a 2012 ya maimaita kansa
- Jihohin Najeriya 28 ake hasashen zasu fuskanci ambaliya
Ana hasashen mumunan ambaliyar ruwan sama a jihohin Najeriya akalla 28 a bana, sabon rahoton hasashen ambaliya AFO ya nuna.
Ana fitar da wannan rahoto ne a kowani shekara.
Jihohin da aka lissafo sune,Abia, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benue, Cross River, Delta, Ebonyi, Edo, FCT, Gombe, Imo, Jigawa, Kaduna, Kano and Kebbi, Kwara, Lagos, Nasarawa, Niger, Ogun, Oyo, Rivers, Sokoto, Taraba da Zamfara.
Ministan arzikin ruwa, Suleiman Adamu, ya lissafa wadannan jihohi ne ranar Alhamis a taron gabatar da rahoton hasashen ambaliya na shekara-shekara na hukumar ayyukan ruwa a Najeriya (NIHSA), rahoton Daily Trust.
KU KARANTA: Ta yaya mutum zai gane ya dace da daren Lailatul Qadr? Tare da Dr Kabir Asgar
KU KARANTA: Jerin shugabannin kasa 15 mafi yawan albashi a nahiyar Afrika, ciki akwai Buhari
"Wannan shekarar, zamu yi fama da matsaloli guda biyu; na COVID-19 da kuma ambaliyar ruwa kamar yadda akayi hasashe," yace.
"A takaice, rahoton AFO na 2021 ya nuna cewa kananan hukumar 302 a jihohin Najeriya da birnin tarayya ake sa ran fuskantar ambaliya."
"Jihohin dake makwabtaka da tekun Niger da Benue ko shakka babu za'ayi mumunan ambaliya."
Ministan ya ce saboda haka suka shirya don ankarar da yan Najeriya kan abinda ka iya faruwa.
Ya yi kira ga yan Najeriya su taimakawa wadanda wannan iftila'i ya fadama wa.
Asali: Legit.ng