Gwamnoni Sun Gana da Sufetan Yan Sanda Na Ƙasa, Sun Tattauna Muhimman Abubuwa a Kan Tsaro

Gwamnoni Sun Gana da Sufetan Yan Sanda Na Ƙasa, Sun Tattauna Muhimman Abubuwa a Kan Tsaro

- Ƙungiyar gwamnoni NGF ta gana da muƙaddashin sufetan yan sanda na ƙasa, Usman Alƙali Baba, a hedkwatar hukumar dake Abuja

- Shugaban gwamnonin yace sun kawo ziyara ga IGP ɗinne domin su taya shi murnar shiga wannan Ofis, da kuma jajanta masa bisa rashin wasu jami'ansa a dalilin matsalar tsaron ƙasar nan

- Fayemi ya ƙara da cewa bayan taya IGP ɗin murna, mun kuma zo nan mu gana dashi ne kan yadda zamu haɗa kai da rundunar yan sanda domin magance matsalar tsaro

Shugaban ƙungiyar gwamnoni NGF kuma gwamnan jihar Ekiti, Dr. Kayode Fayemi tare da takwaransa na jihar Kebbi, Mr. Abubakar Bagudu, sun gana da muƙaddashin sufetan yan sanda na ƙasa ranar Talata.

KARANTA ANAN: Sanatan APC Ya Caccaki Mutanen Dake Kewaye da Buhari, Yace Babu Mai Iya Ɗaga Murya Don Kareshi

Gwamnonin sun yi wannan ganawa ne da IGP domin tattaunawa kan hanyoyin da gwamnonin zasu taimakawa hukumar yan sanda ta daƙile ƙalubalen tsaron da ake fama dashi, kamar yadda Thisdaylive ta ruwaito.

Gwamnoni Sun Gana da Sufetan Yan Sanda Na Ƙasa, Sun Tattauna Muhimman Abubuwa a Kan Tsaro
Gwamnoni Sun Gana da Sufetan Yan Sanda Na Ƙasa, Sun Tattauna Muhimman Abubuwa a Kan Tsaro Hoto: @Kfayemi
Asali: Twitter

A yayin taron nasu, muƙaddashin sufetan yan sanda, Usman Alƙali Baba, yace da haɗin kan gwamnonin "Yan sanda zasu magance abinda ake ganin bazai magantu ba'.

Gwamnonin sun bayyana cewa sun kawo ziyara hedkwatar yan sandan ne domin su taya sabon sufetan murnar shiga wannan babban ofis.

Sannan kuma su jajanta masa bisa hare-haren da aka kaima wasu jami'an yan sanda a faɗin ƙasar nan.

Shugaban ƙungiyar gwamnonin, Fayemi yace:

"Mun kawo wannan ziyara ne domin mu taya sabon sufeta murna, Kuma hukumar yan sanda tana da babbar rawa da zata iya taka mana a matsayin mu na gwamnoni, waɗannan sune dalilan mu na kawo wannan ziyarar."

KARANTA ANAN: Ya Kamata CBN Ya Biya 100 Miliyan Na Fansar Ɗaliban Greenfield Tun Kafin Lokaci Ya Ƙure, Sheikh Gumi

"Bayan taya sufeta murna, muna kuma yi masa jaje da ta'aziyya bisa rashin wasu jami'an yan sanda a wannan yanayi da muke ciki na ƙalubalen tsaro da yaƙi ci yaƙi cinyewa a ƙasar nan."

"Waɗannan sune jarumai na gaske, waɗanda suka bada rayuwarsu don su kare tamu, saboda haka munzo nan a madadin gwamnoni mu mika ta'aziyyarmu ga IG, sannan mu tattauna kan yadda za'a magance faruwar haka nan gaba."

Shugaban gwamnonin ya kara da cewa, gwamnoni sun bada gudummuwarsu kuma zasu cigaba da taimakawa hukumar yan sanda ta ɓangarori da dama da suka haɗa da; Kuɗi, kayan aiki da kuma wasu shirye-shirye.

A wani labarin kuma Buhari Yayi Allah Wadai da Sabon Harin da Wasu Yan Bindiga Suka Kai Benuwai, Ya Faɗi Matakin da Zai Ɗauka

Shugaba Buhari ya nuna matuƙar rashin jin daɗinsa bisa wasu jerin hare-hare da yan bindiga suka kai jihohin Benuwai da Anambra.

Buhari yayi wannan jawabi ne a cikin wani saƙo da babban mai bashi shawara ta musamman kan harkokin yaɗa labarai, Garba Shehu, ya fitar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel