Rashin Tsaro: Gwamna Bagudu Ya Buƙaci Ƴan Nigeria Su Koma Ga Allah

Rashin Tsaro: Gwamna Bagudu Ya Buƙaci Ƴan Nigeria Su Koma Ga Allah

- Gwamnan Kebbi ya bukaci a tuba ga Allah sannan a dage da addu'a don kawo karshen matsalar tsaro

- Gwamnan ya ce ta hanyar addu'a yan kasa za su iya taimakawa kokarin da gwamnati ke yi don ceto kasar

- Gwamnan ya bayyana haka yayin da ya karbi bakuncin manyan jami'an gwamnati don shan ruwa a fadar gwamnatin jihar Kebbi

Gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu ya shawarci ƴan Nigeria su tuba daga zunuban da suke aikatawa su kuma yi addu'ar kawo karshen matsalolin tsaro a kasar nan, The Nation ta ruwaito.

Babban sakataren yada labaran gwamnan Alhaji Abubakar Dakingari, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Birnin-Kebbi, babban birnin jihar a jiya.

Rashin Tsaro: Gwamna Bagudu Ya Buƙaci Ƴan Nigeria Su Koma Ga Allah
Rashin Tsaro: Gwamna Bagudu Ya Buƙaci Ƴan Nigeria Su Koma Ga Allah. Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An Kama Soja da Harsashi Sama da 2000 a Tashar Mota a Maiduguri

Bagudu ya bayyana haka ne lokacin da ya karbi bakuncin manyan masu rike da mukaman gwamnati, alkalai, yan majalisu da sauran manyan yan siyasa don yin buda bakin azumin Ramadana a gidan gwamnatin jihar, Birnin-Kebbi.

Gwamnan ya ce ya zama wajibi ganin irin muhimmancin da tuba yake da shi ga dan Adam a duniya da lahira.

Ya bukaci yan kasa da su karfafa alakar su da Ubangiji ta hanyar addu'a da ayyukan alheri, yana mai tabbatar da cewa Allah ne kadai zai iya magance matsalar tsaro da ta addabi kasar nan.

"Akwai bukatar kowa ya jajirce da addu'a don ganin karshen matsalolin da suka dabaibaye kasar nan.

KU KARANTA: Abun Al’ajabi: Wata Mata Da Bata San Tana Ɗauke Da Juna Biyu Ba Ta Haihu a Jirgin Sama

"Ina kuma tabbatar da irin kokarin da gwamnati mai ci ke yi don tabbatar da an inganta rayuwar mazauna birni da karkara kuma ina addu'ar Allah ya datar da mu alkhairan sa baki daya," a cewar shi.

Bagudu ya yaba da kokarin shugaba Muhammadu Buhari wajen kokarin ceto kasar daga halin da take shirin fadawa.

A wani labarin daban tsohon mataimakin shugaban kasa Mr Atiku Abubakar, a ranar Litinin, ya zargi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da musgunawa kafafen watsa labarai da yi wa yan kasa barazana idan sun bayyana ra'ayoyinsu.

Atiku ya yi wannan zargin ne cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter @atiku domin bikin ranar Yan Jarida na Duniya.

Ya bayyana cewa idan ana tauye hakkin mutane a mulkin demokradiyya, hakan zai kawo rashin jituwa tsakanin mutane da gwamnatin kasa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel