Da duminsa: An sheke wasu mutum 23 a sabon harin Binuwai

Da duminsa: An sheke wasu mutum 23 a sabon harin Binuwai

- 'Yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun halaka mutum 23 a jihar Binuwai daga yammacin Lahadi zuwa safiyar Litinin

- Kamar yadda aka gano, maharan sun kutsa kauyukan karamar hukumar Gwer ta yamma a jihar Binuwai inda suka dinga barna

- Kauyukan da suka shiga suka kai mabanbantan hari sun hada da Agbanu da Tse Amghem dake kusa da Aondoana

Mutum ashirin da uku aka halaka a hare-hare daban-daban da aka kai yankunan jihar Binuwai tsakanin yammacin ranar Lahadi zuwa safiyar Litinin.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, wasu 'yan bindiga sun halaka mutum 17 a wasu hari biyu mabanbanta da aka kai yankunan karkara na karamar hukumar Gwer ta yamma na jihar.

An gano cewa maharan, wadanda a cikin kwanakin nan suka kutsa kauyukan karamar hukumar, sun shiga garin Agbanu dake kan hanyar Naka-Agagbe a gundumar Saghev daga karfe 6 zuwa 7 na yammacin Lahadi kuma sun kashe rayuka biyu.

KU KARANTA: DSS ta aike muhimmin sako ga masu hana zaman lafiya a Najeriya

Da duminsa: An sheke wasu mutum 23 a sabon harin Binuwai
Da duminsa: An sheke wasu mutum 23 a sabon harin Binuwai. Hoto daga @daily_trust
Asali: UGC

KU KARANTA: 'Yan sanda sun kama harsasai 753 masu matukar hatsari a Abakaliki, za a kai Abia

Ganau sun ce a ranar Litinin lamarin ya faru wurin karfe 5 na asuba inda wasu 'yan bindiga suka shiga Tse Amghem dake kusa da Aondoana a karamar hukumar Gwer ta yamma kuma sun kashe mutum 15, jimilla 17 kenan.

An gano cewa mutane da yawa sun samu raunika kuma an kone gidajen jama'a, lamarin da yasa mazauna kauyen suka tsere.

Wani mazaunin kauyen yace mutane da yawa sun bace kuma wasu da suka samu raunika suna asibiti.

A yayin da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Catherine Anene, tace an kai masu rahoton hare-haren amma har yanzu basu samu bayani dalla-dalla ba.

A wani labari na daban, an samu hargitsi da tashin hankali a yankin Gangare na fitacciyar kasuwar Mile 12 dake karamar hukumar Kosefe na jihar Legas a ranar Juma'a bayan an zargi wani kwamandan 'yan sintiri mai suna Haladu Muhammed da yi wa Annabi batanci.

Daily Trust ta tattaro yadda wasu fusatattun matasa suka zargesa da yin kalaman batanci ga Annabi Muhammad, lamarin da yasa suka kai masa farmaki.

Kafin jami'an tsaro su kaiwa wanda ake zargin dauki, an kone motarsa kuma an farfashe gidansa.

Wani ganau ba jiyau ba mai suna Usman Adam Sarauta, ya tabbatar da cewa matasan sun hada da jami'an tsaron da suka gaggauta zuwa wurin bayan kiransu da aka yi.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel