Wani Gwamnan Nigeria Ya Sake Magana Kan Zargin Boko Haram a Jiharsa

Wani Gwamnan Nigeria Ya Sake Magana Kan Zargin Boko Haram a Jiharsa

- Gwamna Muhammadu Badaru na jihar Jigawa ya ankarar da mutanen jiharsa game da yan Boko Haram

- Bayan taron tsaro da aka yi a gidan gwamnatin Jigawa, Badaru ya umurci mutane su kai wa jami'an tsaro rahoto kan duk wanda ba su yarda da shi ba

- Kwamishinan yan sandan Jigawa Usman Gomna ya shaidawa manema labarai cewa sun samu rahoton zargin yan Boko Haram sun shiga jihar kuma suna bincike

Gwamnan jihar Jigawa, Muhammadu Badaru, a ranar Talata ya ankarar da mutanen jiharsa su rika saka ido kan abubuwan da ke faruwa a garuruwansu bayan rahotannin zargin yan Boko Haram sun fara shiga jihar Bauchi da ke makwabta da Jigawa.

A baya-bayan nan, gwamnatin jihar Bauchi ta sanar da cewa yan Boko Haram daga jihar Yobe sun shigo kananan hukumomi hudu a jihar wadda duk suna da iyakoki da Jigawa.

Boko Haram: Wani Gwamnan a Nigeria Ya Sake Ankarar Da Mutanen Jiharsa
Boko Haram: Wani Gwamnan a Nigeria Ya Sake Ankarar Da Mutanen Jiharsa. Hoto: @SankaraJgh
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An Kama Soja da Harsashi Sama da 2000 a Tashar Mota a Maiduguri

Sakataren gwamnatin jihar Bauchi, Sabiu Baba, yayin taron manema labarai a ranar Litinin ya ambaci wuraren da abin ya shafa kamar haka; Zaki, Gamawa, Darazo da Dambam.

Ya ce zargin ya yi karfi ne sakamakon yunkurin da aka yi na lalata na'urorin kamfanonin sadarwa a Gamawa.

Sakamakon abin da ya faru a Bauchi da ke makwabtaka da Jigawa ya saka Gwamna Badaru ya yi taro da masu sarautun gargajiya, shugabannin kananan hukumomi da hukumomin tsaro a dakin taro da ke gidan gwamnati inda a karshe he bukaci mazauna garin su kai rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba.

KU KARANTA: Da Ɗuminsa: An Damƙe Wanda Ake Zargi da Ɗaukan Nauyin Kai Hare-Hare a Imo

"Batun tsaro a kasar nan yasa aka kira taron. Muna ganin ya kamata kowa ya zage damtse ya saka ido sannan mu yi addu'ar Allah ya tsare kasarmu da Jigawa," in ji Badaru.

Kwamishinan yan sandan jihar, Usman Gomna ya shaidawa manema labarai cewa sun samu bayannan sirri kan wasu da ake zargin yan Boko Haram ne a Gwaram kuma suna bibiyan lamarin.

A wani labarin daban kunji wasu matasa a Daura, a ranar Alhamis 29 ga watan Afrilu sun kaddamar da kungiyar ta goyon bayan Dr Abubakar Bukola Saraki ya fito takarar shugabancin kasa a zaben 2023, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban kungiyar, Abubakar Nuhu Adam, ya ce sun yanke shawarar kafa kungiyar na goyon bayan tsohon shugaban majalisar ya yi takarar shugaban kasa ne saboda abin da ya yi da kuma abubuwan da ya ke yi wa matasa a kasar.

Hon. Adam ya bada misali dokar 'Not Too Young To Run' da aka aiwatar lokacin Saraki na shugabancin majalisa da kuma goyon bayan da ya bawa matasa su yi takarar kwamitin zartawar na jam'iyyar PDP da wasu sauransu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel