Budurwa Ta Fasa Auren Saurayinta Bayan Ya Biya Kusan N1m Na Kudin Aurenta

Budurwa Ta Fasa Auren Saurayinta Bayan Ya Biya Kusan N1m Na Kudin Aurenta

- An caccaki wata budurwa yar Najeriya a shafukan sada zumunta bayan ta fasa aurenta

- Hakan ya kasance ne bayan saurayin ya biya kudin aurenta wanda ya kusa naira miliyan

- ‘Yan Najeriya sun nuna kaduwa game da tsadar kudin auren

Wata 'yar Najeriya tana tsaka da shan suka a dandalin sada zumunta bayan ta fasa aurenta.

Da take bayar da labarin, wata mata da aka bayyana sunanta da Amanda Chisom a shafin Facebook, ta ce matar (wacce ba ta bayyana ainihi kowacece ba) ta aika mata sako kan yadda ta sa saurayin da bashi da karfi ya biya kudin aure kusan miliyan.

KU KARANTA KUMA: Bill Gates, Jeff Bezos da Sauran Manyan Attajirai 3 da Suka Saki Matansu a Tarihi da Arzikinsu

Ta rubuta:

"Don haka wannan budurwar a cikin akwatin sakona a yau ta sanya wannan mutumin wanda ba mai kudi ba ne kashe kusan miliyan don ya aure ta kawai sai ga shi ta fasa auren.

"Me zai faru da kudin da ya kashe a kan dangin ta da ke kwadayayyu saboda idan dan uwana ya zo gida da wannan jerin abubuwan bukata don ya auri 'yar kowa zan tambaye shi idan suna ba da hannayen jari ne da ita. Shin bai kamata ya kai karar ta ba akan karya alkawari. Ta yaya mutum zai zama mugu haka?"

Budurwa Ta Fasa Auren Saurayinta Bayan Ya Biya Kusan N1m Na Kudin Aurenta
Budurwa Ta Fasa Auren Saurayinta Bayan Ya Biya Kusan N1m Na Kudin Aurenta Hoto: Amanda Chisom
Asali: Facebook

Hotunan kudin da aka kashe na auren Amanda da aka wallafa sun fusata mutane da yawa. Akwai waɗanda suka yi tunanin cewa hakan bai dace ba.

Mbamala Tochukwu ya rubuta:

"Baya ga wannan jerin, darajar mace ta gari ba za a iya kayyade shi ba, kana iya siyar da duk abin da ka mallaka don ka aure ta amma lalatacciyar mace, hmmmm. Kar ka yi ko kusa koda sun ba ka ita kyauta da asusun tallafi na dala miliyan."

Loveth Oge yayi sharhi:

"Masu laifi ... ne duka dangin.

"Duk wanda sunansa ya bayyana a wannan takarda dole ne a kama shi kuma su biya kudin daya bayan daya."

Umezulike Desmond-Cruz ya yi martani:

"Idan kun bani irin wannan takardar ...

"Zan yaga shi a gaban dukka magabatan sannan in fadawa wacce zan aura din ta same ni a cikin gidana domin taron gaggawa.

"Sakamakon wancan taron ne zai nuna in zan aure ta ko ba zan yi ba."

KU KARANTA KUMA: Father Mbaka Ya Yi Sabon Hasashe, Ya Bayyana Abinda Zai Faru Ga Gwamnatin Buhari Idan Aka Kai Masa Hari

A wani labarin, bayan takardun saki na Bill da Melinda Gates sun bayyana cewa ma'auratan ba su taba samun matsala ba, mutane da yawa suna mamakin yadda ma'auratan, tare da jarin dala biliyan 130, za su raba kadarorinsu.

Gates, mutum na hudu da ya fi kudi a duniya, ya yi magana a baya game da yadda kowanne cikin yaransa uku za su gaji kusan dala miliyan 10 na dukiyarsa, inji rahoton jaridar SUN.

Asali: Legit.ng

Online view pixel