Dalilin da yasa muka kashe daliban jami'ar Greenfield, Masu garkuwa da mutane

Dalilin da yasa muka kashe daliban jami'ar Greenfield, Masu garkuwa da mutane

- Karon farko, yan bindigan da suka sace dalibai sun yi hira da manema labarai

- Sun caccaki gwamnatin jihar Kaduna bisa kin tattaunawa da yan bindiga

- Yan bindigan sun yi barazanar kashe sauran daliban 17 dake hannunsu

Yan bindigan da sukayi awon gaba da daliban jami'ar Greenfield 22 a jihar Kaduna sun bayyana cewa sun kashe dalibai 5 cikinsu ne don nuna gazawar gwamnati.

Za ku tuna cewa a ranar 20 ga Afrilu yan bindiga suka kai hari jami'ar dake hanyar Kaduna-Abuja kuma suka hallaka mai gadi.

Sun bukaci kudin fansan N800m, amma da aka ki biyansu bayan kwanki uku, suka kashe dalibai 5 cikin 22 da suka sace.

An tsinci gawawwakin daliban a cikin daji.

A hirar da VOA Hausa tayi da shugaban yan bindigan mai suna Sani Idris Jalingo (Baleri), ya ce sun kashe dalibai biyar ne don nunawa duniya cewa gwamnati ta gaza.

"Mun ji kalaman gwamnan jihar Kaduna cewa ba zai biya kudin fansa ba don kada yan ta'adda su sayi makamai," yace.

"Hakazalika ya fadawa iyalinsa cewa ba zai biya kudin fansa ba ko an sace su. Dalilin da yasa muka kashe dalibai shine don mu nuna cewa gwamnatin Najeriya ta gaza."

KU KARANTA: An Kama Soja da Harsashi Sama da 2000 a Tashar Mota a Maiduguri

Dalilin da yasa muka kashe daliban jami'ar Greenfield, Masu garkuwa da mutane
Dalilin da yasa muka kashe daliban jami'ar Greenfield, Masu garkuwa da mutane
Asali: UGC

KU KARANTA: Muna tare da shugaba Buhari, Hedkwatar Soji ta yi watsi da shawaran juyin mulki

A bangare guda, yan bindigan sun yi barazanar kashe sauran dalibai 17 dake hannunsu idan gwamnatin Kaduna bata biya kudin fansa ba.

A hira da shugaban yan bindigan, Sani Idris Jalingo wanda aka fi sani da Baleri, yayi da VOA Hausa, ya ce idan gwamnatin Kaduna ko iyayen yaran basu biya milyan 100 da babura kirar Honda 10 ba nan da ranar Talata, zasu kashe sauran daliban.

Baleri yace akwai dalibai 17 a hannunsa; mata 15 da maza 2 kuma a cikinsu akwai jikan tsohon Sarkin Zazzau, Shehu Idris, mai suna Hamza.

Ya ce iyayen yara sun biyasu kimanin milyan 55 amma sun yi amfani da su wajen sayawa daliban garin kwaki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel