Da duminsa: Nan da Talata za mu kashe sauran, Yan bindigan da suka sace Daliban Jami'ar Greenfield

Da duminsa: Nan da Talata za mu kashe sauran, Yan bindigan da suka sace Daliban Jami'ar Greenfield

- Karon farko, yan bindigan da suka sace dalibai sun yi hira da manema labarai

- Sun bada wa'adi kwana daya kacal na abiyar milyan dari

- Yan bindigan da farko sun bukaci milyan 800 amma yanzu sun sauko

Yan bindigan da suka sace daliban jami'ar Greenfield dake jihar Kaduna sun yi barazanar kashe sauran dalibai 17 dake hannunsu idan gwamnatin Kaduna bata biya kudin fansa ba.

A ranar 20 ga Afrilu, an sace dalibai 22 a makarantar Greenfield dake hanyar Kaduna-Abuja.

Bayan mako guda da sace su, an tsinci gawawwakin biyar cikin daliban bayan yan bindigan sun kashesu.

A hira da shugaban yan bindigan, Sani Idris Jalingo wanda aka fi sani da Baleri, yayi da VOA Hausa, ya ce idan gwamnatin Kaduna ko iyayen yaran basu biya milyan 100 da babura kirar Honda 10 ba nan da ranar Talata, zasu kashe sauran daliban.

Baleri yace akwai dalibai 17 a hannunsa; mata 15 da maza 2 kuma a cikinsu akwai jikan tsohon Sarkin Zazzau, Shehu Idris, mai suna Hamza.

Ya ce iyayen yara sun biyasu kimanin milyan 55 amma sun yi amfani da su wajen sayawa daliban garin kwaki.

Ya lashi takobin cewa wannan shine gargadinsa na karshe kuma idan gwamnati da iyayen yara suka ki biyan kudin, zai kashe dukkan daliban.

"Bayan kudi milyan 100, da Honda Boko Haram kwara 10 da za'a kawo mana, idan aka kawo gobe zasu koma, idan ba'a kawo ba ranar Talata za'a ga gawawwakinsu, sai an zo da tirela a kwasa," yace.

DUBA NAN: Nasihohi guda 50, Daga Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Kano

Da duminsa: Nan da Talata za mu kashe sauran, Yan bindigan da suka sace Dalibai Jami'ar Greenfield
Da duminsa: Nan da Talata za mu kashe sauran, Yan bindigan da suka sace Dalibai Jami'ar Greenfield
Asali: Original

DUBA NAN: Waiwaye: Yadda El-Rufai Ya Nemi Jonathan Ya Tattauna Kan Sakin 'Yan Matan Chibok

A bangare guda, gwamnatin kaduna tayi Allah wadai da kisan wasu ɗalibai dake karatu a manyan makarantun gaba da sakandire da yan bindiga keyi a jihar.

A wani jawabi da kakakin gwamnan jihar, Muyiwa Adekeye, ya fitar ranar Talata, ya jajantawa iyalan da abun ya shafa, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Adekeye yace: "Wannan kisan matasan da masu garkuwa da mutanen keyi wani ɓangarene na ƙoƙarin su yaudari gwamnati."

"Kuma suna aikata wannan mummunan ta'addancin ne domin su saka gwamnatin Kaduna ta canza matsayar daga 'Ba biyan kudin fansa, ba tattaunawa' zuwa yadda suke so."

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng