'Yan Bindiga Sun Kashe Kwamishina, Sun Sace Shugaban Ƙaramar Hukuma a Kogi

'Yan Bindiga Sun Kashe Kwamishina, Sun Sace Shugaban Ƙaramar Hukuma a Kogi

- Rundunar yan sanda reshen jiar Kogi ta tabbatar da kashe Mr Solomon Akeweje da sace Mr Pius Kolawale

- An sace mutanen biyu ne bayan da wasu yan bindiga suka kai wa motarsu hari a ranar Asabar a Eruku

- Solomon Akewaje kwamishina ne a jihar Kogi yayin da Pius Kolawole shugaban karamar hukuma ne a Kogi

Yan bindiga sun kashe kwamishina a hukumar Fansho ta jihar Kogi, Mr Solomon Akeweje sannan sun sace shugaban karamar hukumar Yagba ta Yamma, Mr Pius Kolawole, The Nation ta ruwaito.

Kakakin rundunar yan sandan jihar, DSP William Aya, ya tabbatar da hakan inda kwamishinan da Kolawole suna cikin mota daya ne a yayin da yan bindigan suka kai musu hari.

'Yan Bindiga Sun Kashe Kwamishina, Sun Sace Shugaban Ƙaramar Hukuma a Kogi
'Yan Bindiga Sun Kashe Kwamishina, Sun Sace Shugaban Ƙaramar Hukuma a Kogi. Hoto: @Vangaurdngrnews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Jerry Gana Ya Yi Barazanar Maka Majalisar Ƙolin Musuluncin Nigeria a Kotu

Ya ce yan sanda sun samu rahoton kai harin misalin karfe 4.30 na yamma a ranar Asabar 1 ga watan Mayu kuma nan take suka garzaya inda abin ya faru.

Mai magana da yawun yan sandan ya ce an kaiwa wadanda abin ya faru da su hari ne a Eruku, wani gari da ke kan iyakan jihar Kwara da Kogi.

A cewar Iya, Akeweje da Kolawole suna hanyarsu ta komawa Egba ne daga jihar Kwara inda yan bindigan da ba san ko su wanene ba suka kai musu hari.

KU KARANTA: Gwamna Zulum Ya Miƙa Gwamnatin Jihar Borno Ga Usman Kadafur

Ba a san inda Kolawole da aka sace ba yake a halin yanzu kuma wadanda suka sace shi ba su tuntubi kowa ba.

Amma, direban motar ya tsira da ransa yayin da aka kai gawar Akeweje asibitin ECWA da ke Egbe.

A wani labarin daban kunji wasu matasa a Daura a ranar Alhamis 29 ga watan Afrilu sun kaddamar da kungiyar ta goyon bayan Dr Abubakar Bukola Saraki ya fito takarar shugabancin kasa a zaben 2023, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban kungiyar, Abubakar Nuhu Adam, ya ce sun yanke shawarar kafa kungiyar na goyon bayan tsohon shugaban majalisar ya yi takarar shugaban kasa ne saboda abin da ya yi da kuma abubuwan da ya ke yi wa matasa a kasar.

Hon. Adam ya bada misali dokar 'Not Too Young To Run' da aka aiwatar lokacin Saraki na shugabancin majalisa da kuma goyon bayan da ya bawa matasa su yi takarar kwamitin zartawar na jam'iyyar PDP da wasu sauransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164