Kayatattun Hotunan katafaren filin jiragen sama na China ya bar mutane baki bude
- China ta kai kololuwa a fasahar zamani inda ta gina katafaren filin sauka da tashin jiragen sama na tiriliyan N6.4
- Gagarumin filin jiragen saman na da hanyar wucewan jiragen sama hudu a lokaci daya kuma yana da dakin motsa jiki
- 'Yan Najeriya sun gigice tare da yin tsokaci kala-kala bayan ganin hotunan inda suka bayyana su da ababen mamaki
Hotunan sabon tarihin da kasar China ta kafa bayan ta gina katafaren filin sauka da tashin jiragen sama ya gigita jama'a a kafar sada zumuntar zamani.
A wani hoto da @kingtundeednut ya wallafa a shafinsa na Instagram, kasar dake nahiyar Asia ta yi ginin filin sauka da tashin jiragen saman a fili mai girman 700.00m².
Gagarumin filin jirgin saman na nan shinfide a babban fili mai girman kafa 7.5 miliyan wanda daidai yake da fiilayen kwallo 98 kuma yana nan a iyakan Beijing da Langfang, kamar yadda Wikipedia ta bayyana.
KU KARANTA: Muhimmiyar Sanarwan da CBN ta baiwa ma'aikatanta ya tada hankalin mazauna Abuja
KU KARANTA: Da duminsa: IGP ya sauyawa manyan 'yan sandan kudu maso gabas wurin aiki
Filin jirgin da ya hadiya N6.4 tiriliyan an saka masa suna Daxing International Airport, Beijing. Yana da wurin wucewar jiragen sama 4 a lokaci daya, dakin motsa jiki, fasahar yanar gizo ta 5G da sauransu.
An gano cewa za a kara wurin wucewar jiragen sama uku nan gaba kadan, wanda zai mayar da shi 7 a lokaci daya.
Wasu 'yan Najeriya da suka ga wannan gagarumin ci gaban, sun ce China suna rayuwa ne a karni na daban. Wasu kuwa sun matukar firgita da yanayin tsarin wurin.
A wani labari, fadar shugaban kasa tace Ejike Mbaka, shugaban Adoration Ministry (AMEN), ya taba kawai shugaban kasa 'yan kwangila uku amma aka dakatar da shi.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, yace Mbaka ya makance da har ya bukaci shugaban kasa ya yi murabus sakamakon tsanantar matsalar tsaro a kasar nan.
A wata takarda da ya fitar a ranar Juma'a, Shehu yace akwai matukar abun mamaki ta yadda wanda ya goyi bayan shugaban kasan har sau biyu a yau ya sauya ya koma yana neman yayi murabus ko a tsige shi.
Asali: Legit.ng