Mbaka ya bukaci kwangila bayan goyon bayan Buhari amma aka hana shi, Garba Shehu

Mbaka ya bukaci kwangila bayan goyon bayan Buhari amma aka hana shi, Garba Shehu

- Malam Garba Shehu ya fallasa dalilin da yasa Mbaka ya bukaci shugaban kasa yayi murabus a kan rashin tsaro da ya addabi kasar nan

- Shehu yace Mbaka ya kaiwa Buhari 'yan kwangila uku har fadar shugaban kasan amma Buhari ya bukaci su bi hanyar da ta dace

- A cewar mai magana da yawun shugaban kasan, babu yadda za a yi wanda ya goyi bayan shugaban kasan har sau biyu, a yau ya zama makiyinsa

Fadar shugaban kasa tace Ejike Mbaka, shugaban Adoration Ministry (AMEN), ya taba kawai shugaban kasa 'yan kwangila uku amma aka dakatar da shi.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, yace Mbaka ya makance da har ya bukaci shugaban kasa ya yi murabus sakamakon tsanantar matsalar tsaro a kasar nan.

A wata takarda da ya fitar a ranar Juma'a, Shehu yace akwai matukar abun mamaki ta yadda wanda ya goyi bayan shugaban kasan har sau biyu a yau ya sauya ya koma yana neman yayi murabus ko a tsige shi.

KU KARANTA: Tsaron kasa: Buhari ya fusata, yace Ortom baya ganin laifin kansa, na wasu yake hange

Mbaka ya bukaci kwangila bayan goyon bayan Buhari amma aka hana shi, Garba Shehu
Mbaka ya bukaci kwangila bayan goyon bayan Buhari amma aka hana shi, Garba Shehu. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Baƙin mutum ya mayarwa baturiya miliyan 13 da ƴan damfara suka tura asusun bankinsa

"Ga dalla-dalla: Mbaka ya bukaci ganawa da shugaban kasa amma kuma sai ya zo tare da 'yan kwangila uku. Shugaban kasan ya barsu sun ganshi amma abun mamaki sai Mbaka ya bukaci a basu kwangila domin biyansa goyon bayan da ya nunawa Buhari.

"Duk wanda ya san shugaban kasa Buhari ya san shi da rashin son karya dokoki ballantana a mu'amala da 'yan kwangila. Ya bukaci hukumomin da suka dace su duba lamarin kamar yadda doka ta tsara," yace.

A wani labari na daban, shugaban dakarun sojin kasa, Laftanal Janar Ibrahim Attahiru ya jaddada cewa rundunar sojin kasa ta mayar da hankali wurin ganin bayan 'yan ta'addan Boko Haram a yankin arewa maso gabas.

A yayin jawabi ga manema labarai a jihar Borno a ranar Alhamis, yace ya je duba Rundunar Operation Lafiya Dole ne dake Maidguri domin ziyartar sojojin da suka samu raunika.

A yayin tabbatar da cewa dakarun sun mayar da hankali wurin shawo kan matsalar tsaro kamar 'yan bindiga da satar mutane, daga cikin miyagun al'amuran da kasar nan ke fuskanta, Attahiru yace babu yadda za a yi dakarun su ce sun samu nasara ta karya kamar yadda wasu suke zarginsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel