Baƙin mutum ya mayarwa baturiya miliyan 13 da ƴan damfara suka tura asusun bankinsa

Baƙin mutum ya mayarwa baturiya miliyan 13 da ƴan damfara suka tura asusun bankinsa

- Wani bakar fata mai suna Joseph James Nantomah, ya ceci wata baturiya inda ya mayar mata kudinta da aka damfareta

- James ya bayyana cewa an sako masa kudinta ne zuwa asusun bankinsa wanda daga bisani 'yan damfaran suka ce ya tura masu

- Yayin da jama'a da yawa suke kwarzanta abin arzikin da yayi, wasu kuwa tambaya suke yadda 'yan damfaran suka samu bayanan asusun bankinsa

Wani bakar fata mai suna Joseph Nantomah ya je shafinsa na Instagram inda ya bayyana yadda ya taimaki wata baturiya ta samo kudadenta daga wasu 'yan damfara.

A wata wallafa da yayi a ranar Laraba, 28 ga watan Afirilun 2021, mutumin yace ya yi tukin sa'o'i domin ya kai mata miliyan 13 da aka tura asusun bankinta.

KU KARANTA: Yadda na hadu da matsafin tsoho mai shekaru 67 a yawon barbadata, Budurwa

Baƙin mutum ya mayarwa baturiya miliyan 13 da ƴan damfara suka tura asusun bankinsa
Baƙin mutum ya mayarwa baturiya miliyan 13 da ƴan damfara suka tura asusun bankinsa. Hoto daga @theblackmentor
Asali: Instagram

KU KARANTA: 'Yan sanda sun kai samame maboyar 'yan bindiga a Benue, sun sheke 3

Ya bayyana cewa bayan an sako masa kudin asusun bankinsa, 'yan damfaran sun kira shi inda suka tambaye shi kudin.

Da ya ki bin umarninsu, sai da yayi tukin sa'o'i bakwai daga Wisconsin zuwa Indiana don ya kaiwa matar kudinta.

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin:

Joshe4u yace: "Allah yayi maka albarka dan uwana a kan wannan kokarin da kayi domin dawo da sunan Najeriya. Allah ya kara maka budi."

atuanyachigozie cewa tayi: "Ka yi abin arziki dan uwa... Allah ya albarkaceka."

ugezujugezu yace: "Ka yi abin mamaki dan uwa. Chukwu Okike Abiama zai biyaka ta inda baka tsammani."

A wani labari na daban, Sanata Clifford Ordia yayi kira a kan garambawul a fannin tsarin tsaron kasar nan bayan 'yan bindiga sun kai masa farmaki har sau biyu a cikin sa'o'i 24 a wata tafiya da yayi.

'Yan bindigan sun kaiwa sanatan mai wakiltar Edo ta tsakiya farmaki har sau biyu a ranar Litinin a kan babban titin Okene zuwa Lokoja da kuma titin Lokoja zuwa Abuja, Daily Trust ta wallafa.

Ordia wanda ke shugabantar kwamitin majalisar dattawan a harkokin bashin cikin gida da waje, ya sanar da manema labarai a garin Abuja cewa an sakarwa tawagarsa ruwan wuta yayin da yake komawa Abuja daga garinsu na Edo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng