Gwamnatin Tarayya Za Ta Kori Ma'aikata Da Ba Su San Makamashin Aiki Ba

Gwamnatin Tarayya Za Ta Kori Ma'aikata Da Ba Su San Makamashin Aiki Ba

- Gwamnatin tarayya ta nuna alamar tana shirin korar ma'aikata da ba su san makamashin aiki ba

- Folashade Yemi-Esan, shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya ce ta sanar da hakan ranar Alhamis 29 ga watan Afrilu

- Shugaban ma'aikatan na kasa ta ce wadanda suka cancanta ne kawai za a dauka aiki a hukumomin gwamnatin tarayya

Folashade Yemi-Esan, shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya, HoS, ta ce za a bullo da tsarin da zai tabbatar wadanda suka dace ne kawai za su samu aikin gwamnatin tarayya.

Vanguard ta ruwaito cewa Yemi-Esan ta yi wannan furucin ne a wurin taron Hukumar Yin Sauye-Sauye a ayyukan gwamnati, BPSR, da aka yi a ranar Alhamis 29 ga watan Afrilu a Abuja.

DUBA WANNAN: Dangote da Alakija sun shiga jerin ƴan Nigeria da suka fi kyauta a 2021

FG Za Ta Kori Ma’aikata Da Ba Su San Makamashin Aiki Ba, Ta Bada Dalili
FG Za Ta Kori Ma’aikata Da Ba Su San Makamashin Aiki Ba, Ta Bada Dalili. Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Ta ce akwai bukatar a yi waje da wadanda ba su san makamashin aiki ba.

Emmanuel Meribole, Sakataren dindindin na bangaren tsare-tsare a ofishin na HoS ne ya wakilci Yemi-Esan a wurin taron.

DUBA WANNAN: 2023: Ahmed Musa, Tuface da Omotola sun samu tikitin takara kyauta a ADC

A cewarta, a halin yanzu gwamnatin tarayya ba hukuma bace da za a rika daukan ko wane irin mutane aiki domin magance matsalar rashin ayyuka a kasar.

HoS din ta ce aikin gwamnatin tarayya na kan tsari ne na magance matsalar tattalin arziki, zamantakewa da muhalli na SDGs.

Shugaban BPSR, Dasuki Arabi ya ce bayan annobar COVID-19, ana bukatar aiwatar da sabon tsarin aikin gwamnati na zamani da gwamnatin tarayya ta tsara.

A wani labarin daban kunji wasu matasa a Daura a ranar Alhamis 29 ga watan Afrilu sun kaddamar da kungiyar ta goyon bayan Dr Abubakar Bukola Saraki ya fito takarar shugabancin kasa a zaben 2023, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban kungiyar, Abubakar Nuhu Adam, ya ce sun yanke shawarar kafa kungiyar na goyon bayan tsohon shugaban majalisar ya yi takarar shugaban kasa ne saboda abin da ya yi da kuma abubuwan da ya ke yi wa matasa a kasar.

Hon. Adam ya bada misali dokar 'Not Too Young To Run' da aka aiwatar lokacin Saraki na shugabancin majalisa da kuma goyon bayan da ya bawa matasa su yi takarar kwamitin zartawar na jam'iyyar PDP da wasu sauransu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel