Rashin tsaro: Sabon IGP ya yi zaman kus-kus tare da wasu Gwamnonin Jihohi 2 a hedikwata

Rashin tsaro: Sabon IGP ya yi zaman kus-kus tare da wasu Gwamnonin Jihohi 2 a hedikwata

- Dr. Kayode Fayemi da Sanata Atiku Abubakar Bagudu sun kai wa IGP ziyara jiya

- Gwamnonin sun bayyana makasudin zuwansu wajen sabon Sufetan ‘Yan Sandan

- Manyan Gwamnonin su na neman hanyar da za a kawo karshen matsalar tsaro

Mai girma gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi da takwaransa na jihar Kebbi, Sanata Atiku Abubakar Bagudu, sun zauna da shugaban ‘yan sanda na kasa.

Jaridar Daily Trust ta ce gwamnonin biyu sun yi zama da mukaddashin shugaban ‘yan sandan Najeriya, IGP Usman Baba da nufin shawo kan matsalar tsaro.

Dr. Kayode Fayemi shi ne shugaban kungiyar gwamnoni na kasa, a yayin da Atiku Abubakar Bagudu ya ke rike da kujerar shugaban gwamnonin jam’iyyar APC.

KU KARANTA: Babu bukatar maganar zaben 2023 muddin babu zaman lafiya - PDP

A wajen wannan taro, IGP Usman Baba ya sanar da gwamnonin cewa idan jihohi su ka bada hadin-kai, za a kawo karshen wannan matsala, a samu zaman lafiya.

Kamar yadda su ka bayyana, gwamnonin sun ce sun ziyarci hedikwatar ‘yan sanda ne domin taya Usman Baba murnar zama sabon sufetan ‘yan sandan Najeriya.

Bayan haka, gwamnonin sun jajanta wa babban jami’in tsaron a kan rashin wasu jami’ai da ya yi.

Gwamnonin biyu sun kuma bayyana cewa ziyararsu ta na da nasaba da neman hadin-kan ‘yan sanda domin ganin yadda za a kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Rashin tsaro: Sabon IGP ya yi zaman kus-kus tare da wasu Gwamnonin Jihohi 2 a hedikwata
Gwamnonin Jihohin APC a Aso Villa
Asali: Facebook

KU KARANTA: Ortom ya fusata Buhari, Shugaban kasa ya maida martani

“Ziyara ce ta a-kai-a-kai, ba mu samu damar gana wa da sabon IGP tun da ya shiga ofis ba.”

“Bayan zuwa mu taya shi murna, mu na kuma so mu aika masa da sakon ta’aziyyarmu na wasu jami’ai da aka kashe, wannan lamari abin takaici ne.” inji gwamnan Ekiti.

Fayemi ya ce: “A matsayinmu na gwamnoni, mun zo ne mu yi ta’aziyya, mu kuma yi tunanin hanyar da za a bijiro wa matsalar rashin tsaro da ya yi kamari a kasarmu.”

Fitaccen Faston Katolika, Ejika Mbaka ya bukaci majalisa su taru su sauke shugaban kasa Muhammadu Buhari idan har shugaban kasar ba zai sauka daga kan kujera ba.

Faston da ya yi wa Goodluck Jonathan adawa a 2015, ya ce ‘Ubangiji ya yi fushi da Buhari’. Mbaka ya koka kan yadda ake hallaka Bayin Allah, amma shugaban kasar ya yi gum.

Asali: Legit.ng

Online view pixel