Boko Haram: Ndume Ya Tona Daga Inda Yan Ta’adda Ke Samun Makamai da Alburusai

Boko Haram: Ndume Ya Tona Daga Inda Yan Ta’adda Ke Samun Makamai da Alburusai

- Sanata Ali Ndume ya bayyana daga inda ‘yan kungiyar Boko Haram ke samun makamansu

- A cewar tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar dattawan, masu tayar da kayar bayan suna sace makamai da alburusai daga sojoji da hukumomin tsaro

- Ndume ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka watsa a ranar Alhamis, 29 ga Afrilu

Sanata Ali Ndume, shugaban kwamitin majalisar dattijai a kan Sojoji, ya magantu a kan tushen makaman Boko Haram da ake yawan amfani da su don aiwatar da ta'addanci.

Ndume ya yi ikirarin cewa yawancin makamai da alburusai da maharan ke yin amfani da su an sace su ne daga wajen sojojin Najeriya, rundunar tsaro, da sauran hukumomin tsaro.

Dan majalisar, wanda ke wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattijai, ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talbijin din Channels TV Politics Today wanda aka watsa a ranar Alhamis, 29 ga Afrilu.

Boko Haram: Ndume Ya Tona Daga Inda Yan Ta’adda Ke Samun Makamai da Alburusai
Boko Haram: Ndume Ya Tona Daga Inda Yan Ta’adda Ke Samun Makamai da Alburusai Hoto: @Malindume
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Obaseki da Wani Gwamnan Arewa Sun Samu Babban Mukami a PDP Gabannin Zaben Shugaban Kasa Na 2023

A cewarsa, masu tayar da kayar bayan suna kan neman kayan yaki da alburusai bayan shugaban sojojin ya kunna musu wuta. Ya ci gaba da bayanin cewa ‘yan ta’addan kuma suna samun makamai daga Libya da Chadi.

Lokacin da aka tambaye shi ko ‘yan ta’addan da suka mamaye wasu yankuna na arewa maso gabas koma baya ne, Ndume ya ce ba haka bane. Ya bayyana cewa masu tayar da kayar bayan sun rike garuruwan ne sakamakon karancin sojoji a kasa.

Da yake ci gaba da magana, dan majalisar ya bayyana cewa kungiyar ta'addancin ba ta rike wani gari har abada.

KU KARANTA KUMA: Kashe-Kashe: Daga Karshe Tinubu Ya Yi Magana, Ya Aika Gagarumin Sako Ga Yan Najeriya

A wani labarin, mambobin ƙungiyar Boko Haram sun ƙwace iko da gonaki da kuma ayyukan gona a garin Geidam, jihar Yobe kamar yadda Punch ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa yan ta'addan, waɗanda suka kori mafi yawancin mutanen garin, sun fara yiwa mutanen da suka rage wa'azi akan jihadi, sannan kuma suna basu kyautar kuɗi.

Gambo Abdullahi, wani ɗan asalin garin Geidam dake zama a Damaturu, yace har yanzun garin na hannun yan ta'adda yayin da sojojin Najeriya na can yammacin garin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel