Obaseki da Wani Gwamnan Arewa Sun Samu Babban Mukami a PDP Gabannin Zaben Shugaban Kasa Na 2023

Obaseki da Wani Gwamnan Arewa Sun Samu Babban Mukami a PDP Gabannin Zaben Shugaban Kasa Na 2023

- Jam’iyyar PDP ta kaddamar da wani kwamiti na yin rajista kafin zaben 2023

- Kwamitin zai kula da rijistar na yanar gizo da za a yi wa mambobin jam’iyyar PDP a fadin Najeriya

- Gwamna Godwin Obaseki da gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri, za su sa ido kan ayyukan sabuwar kungiyar

A shirye-shiryen farko na babban zaben 2023, Jam’iyyar PDP ta yi nade-nade biyu masu muhimmanci.

Jam’iyyar adawar a ranar Alhamis, 29 ga Afrilu, ta nada Gwamna Godwin Obaseki na Edo a matsayin shugaban sabon kwamitinta na rajista.

KU KARANTA KUMA: Kashe-Kashe: Daga Karshe Tinubu Ya Yi Magana, Ya Aika Gagarumin Sako Ga Yan Najeriya

Obaseki da Wani Gwamnan Arewa Sun Samu Babban Mukami a PDP Gabannin Zaben Shugaban Kasa Na 2023
Obaseki da Wani Gwamnan Arewa Sun Samu Babban Mukami a PDP Gabannin Zaben Shugaban Kasa Na 2023 Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

A shafinta na Twitter a ranar Alhamis, jam’iyyar ta kuma nada gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, a matsayin mataimakin shugaban kwamitin.

Majalisar Zartarwar babbar jam’iyyar adawar ta Kasa (NEC) ce ta yanke wannan shawarar.

Ya sanar:

"... @OfficialPDPNig NEC ta ambaci gwamnan jihar Edo @GwamnaObaseki a matsayin shugaban kwamitin rajista. Gwamnan jihar Adamawa, @AhmaduFintiri zai zama mataimakin shugaban kwamitin."

KU KARANTA KUMA: Boko Haram Ta Kai Hari Kan Sansanin Soji A Borno, Ta Lalata Komai, Cewar Rahoto, Sojoji Sun Maida Martani

A gefe guda, mun ji cewa bayan zargin da aka jefe shi da shi a makon da ya gabata na cewa akwai hannunsa a badakalar cin Naira biliyan 10, Prince Uche Secondus ya kai maganar kotu.

A ranar Alhamis, shugaban PDP na kasa, Prince Uche Secondus, ya kai karar Kassim Afegbua, ya na neman kotu ta tursasa shi ya janye zargin da ya jefe shi da shi.

Bayan janye kalaman da ya yi, shugaban PDP na kasa ya nemi Kassim Afegbua ya biya kudi har Naira biliyan 1 a sakamakon bata masa suna da ci masa zarafi da ya yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel