Babu wanda ya tsira a kasar nan, Sanata Ordia bayan ya tsallake hari 2 cikin sa'a 24

Babu wanda ya tsira a kasar nan, Sanata Ordia bayan ya tsallake hari 2 cikin sa'a 24

- Sanata Ordia mai wakiltar Edo ta tsakiya yayi kira ga gwamnatin tarayya da tayi garambawul ga tsarin tsaro a kasar nan

- Wannan yana zuwa ne bayan kaiwa sanatan farmaki da 'yan bindiga suka yi har sau biyu a cikin sa'o'i 24

- Ordia ya tabbatar da cewa babu wanda ya tsira a kasar nan bayan 'yan sanda uku dake tare dashi sun matukar jigata

Sanata Clifford Ordia yayi kira a kan garambawul a fannin tsarin tsaron kasar nan bayan 'yan bindiga sun kai masa farmaki har sau biyu a cikin sa'o'i 24 a wata tafiya da yayi.

'Yan bindigan sun kaiwa sanatan mai wakiltar Edo ta tsakiya farmaki har sau biyu a ranar Litinin a kan babban titin Okene zuwa Lokoja da kuma titin Lokoja zuwa Abuja, Daily Trust ta wallafa.

Ordia wanda ke shugabantar kwamitin majalisar dattawan a harkokin bashin cikin gida da waje, ya sanar da manema labarai a garin Abuja cewa an sakarwa tawagarsa ruwan wuta yayin da yake komawa Abuja daga garinsu na Edo.

Yace harin farko ya faru ne a kan hanyar Okene zuwa Lokoja a Kogi, yayin da na biyun ya faru a Abaji, Abuja duk a ranar Litinin.

KU KARANTA: Rashin tsaro: Ka yafewa 'yan Najeriya da suka dinga zaginka, J. Martins ga Jonathan

Babu wanda ya tsira a kasar nan, Sanata Ordia bayan ya tsallake hari 2 cikin sa'a 24
Babu wanda ya tsira a kasar nan, Sanata Ordia bayan ya tsallake hari 2 cikin sa'a 24. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Rashin tsaro: Tinubu ya gana da Buhari, yace babu shugaban kasan da zai so a gurgunta kasarsa

Yace jami'an tsaron dake tare da shi ne suka budewa 'yan ta'addan wuta. Daga nan ne ya tsere ba tare da wani rauni ba amma motarsa ta sha ruwan harsasai. Dan majalisar yace uku daga cikin jami'an tsaron dake tare dashi sun jigata.

Daya daga cikin 'yan sandan da suka jigata yana cikin mummunan hali, amma kuma ana bashi taimakon masana lafiya a wani asibiti dake Abuja, ya kara da cewa.

Yace: "Muna tahowa daga jihar Edo, nan wurin Okene zuwa Lokoja ne muka hadu da 'yan bindiga. Sun budewa tawagata wuta amma zakakuran 'yan sandan sun mayar da martani.

"A yayin musayar wutan, uku daga cikin 'yan sandan sun samu rauni inda daya daga cikin yake cikin mawuyacin hali. An mika shi FMC Lokoja dake jihar Kogi."

Yayi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta kawo salon garambawul ga tsarin tsaron kasar nan inda ya ja kunnne tare da cewa babu wanda ya tsira yanzu.

A wani labari na daban, fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, yayi kira ga gwamnatin tarayya da ta kawo karshen matsalar tsaron da ta addabi kasar nan, inda yace babu wanda ta tsallake.

Babban malamin yace hakkin gwamnati ne kare 'yan kasa daga 'yan bindiga da sauran miyagun da suka addabesu, Daily Trust ta wallafa.

Sheikh Dahiru Bauchi ya yi wannan tsokacin ne bayan karbar wakilan Kiristoci da yayi wanda suka samu jagorancin tsohon ministan wasanni, Solomon Dalung da kuma Fasto Yohana Buru na Peace Revical and Reconciliation of Nigeria dake gidansa na Kaduna a ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel