Yan kungiyar IPOB sun sayi bama-bamai, suna shirin fara kai hare-hare: DSS

Yan kungiyar IPOB sun sayi bama-bamai, suna shirin fara kai hare-hare: DSS

- Yan kungiyar IPOB sun fara safarar bama-bamai don kai hare-hare, DSS ta bankado

- Hukumar ta ankarar da shugaban Sojojin dake jihar Imo

- Wannan ya biyo bayan hare-haren da yan ta'addan ke kaiwa jami'an tsaro a jihar

Hukumar tsaron farin kaya DSS ta ce yan kungiyar IPOB da hukumar tsaron da suka kafa ESN sun sayi bama-bamai da suke niyyar tayar da tarzoma da su a jihar Imo.

Hukumar ta ce ta samu labarin leken asiri cewa yanzu haka ana tafiyar da bama-baman dake jihar Legas zuwa karamar hukumar Orlu, a jihar Imo, The Punch ta ruwaito.

DSS ta bayyana hakan ne a wasikar da ta aikewa Kwamandan Artillery Brigade, Obinze, Owerri, Imo.

I. Abdullah ya rattaba hannu kan wasikar mai lamba S.238/5/1538 da ranan wata 26 ga Afrilu, 2021, a madadin Diraktan DSS na jihar Imo.

KU KARANTA: Shahrarren Dan bindigan da ya tuba, Auwalu Daudawa, ya koma gidan jiya

Yan kungiyar IPOB sun sayi bama-bamai, suna shirin fara kai hare-hare: DSS
Yan kungiyar IPOB sun sayi bama-bamai, suna shirin fara kai hare-hare: DSS
Asali: UGC

DUBA NAN: Matsalar tsaro: Lokacin tsige Buhari bai yi ba, Sanatan da yan bindiga suka addabi mazabarsa

Wani sashen wasikar yace: "Bayanan leken asiri sun nuna cewa haramtacciyar kungiyar IPOB/ESN ta sayi bama-bamai domin cigaba da kai hare-hare."

"An samu tabbacin cewa an fara tafiyar da wadannan sabbin bama-bamai daga Legas zuwa wani waje a karamar hukumar Orlu."

"Manyan motoci ake amfani da su wajen tafiyar da makaman domin gujewa jami'an tsaro a hanya. Hakazalika an tattaro cewa kungiyar na shirin amfani da bama-baman wajen kai hare-hare dukiyoyin gwamnati da ofishoshin jami'an tsaro a jihar.

Hukumar DSS, saboda haka, ya shawarci kwamandan ya tabbatar da cewa an tura jami'an tsaro domin binciken duk wani babbar motar dake shirin shiga jihar.

A bangare guda, Shahrarren dan bindigan da ya jagoranci satan daliban Kankara 300, Auwalu Daudawa, ya koma daji bayan kimanin watanni uku da alanta tubarsa daga barandancin da satar mutane.

A cewar Daily Trust, wata majiyar jami'an tsaro da wasu majiyoyi na kusa da dan bindigan sun tabbatar da cewa Auwalu Daudawa ya koma dajin dake da iyaka da jihar Katsina.

Auwalu Daudawa ne ya jagoranci satan daliban makarantar GSS Kankara ranar 12 ga Disamba, 2020.

Asali: Legit.ng

Online view pixel