Boko Haram ta raba wasika, ta sanar da dalilin kai miyagun hare-hare a Najeriya

Boko Haram ta raba wasika, ta sanar da dalilin kai miyagun hare-hare a Najeriya

- A yayin da 'yan Boko Haram ke kai miyagun hare-hare a Geidam, sun raba wasiku ga mazauna wurin

- Kamar yadda wasikun suka bayyana, 'yan Boko Haram sun ce Jihadi suke tabbatarwa a kan sojojin Najeriya

- Kungiyar ta'addancin tace ta bayyana cewa hatta wadanda ke goyon bayan sojojin Najeriya sai sun ga bayansu

Bayan miyagun hare-haren da 'yan Boko Haram suka kai a garin Geidam dake jihar Yobe a ranar Juma'a, 23 ga watan Afirilu, sun raba wasika ga mazauna yankin yayin harin.

A yayin bada dalilin da yasa suke kaiwa 'yan Najeriya hari, kungiyar 'yan ta'addan a wasikar ta bayyana cewa Boko Haram ta zo yin jihadi ne da rundunar sojin Najeriya.

A karin bayani, an rubuta wasikar a harshen Hausa kuma a wasikar an jaddada cewa sun fito ne domin halaka duk wani wanda ke hana Jihadi ko kuma yake aiki tare da hukumar tsaron Najeriya.

KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun babbaka fadar Igwe Ifitedunu dake Anambra

Boko Haram ta raba wasika, ta sanar da dalilin kai miyagun hare-hare a Najeriya
Boko Haram ta raba wasika, ta sanar da dalilin kai miyagun hare-hare a Najeriya. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

KU KARANTA: Sunday Igboho ya sha da kyar yayin da 'yan bindiga suka kai farmaki gidansa

Vanguard ta samu wasikar da 'yan Boko Haram suka raba a yankin, wanda a takaiace yace, "Muna fadan Jihadi ne, muna kuma harar rundunar soji, masu hada kai dasu da kuma duka wani wanda zai hana su daga yin Jihadi."

"An bada wasikar ne a rubuce a harshen Hausa kuma na raba su ga mazauna Geidam a yammacin Juma'a kafin su fara aiwatar da harin," wata majiyar ta bayyana.

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya mika ta'aziyyarsa da jajensa ga iyalan sojojin da suka rasu a cikin kwanakin karshen mako yayin yaki da 'yan ta'addan Boko Haram a garin Mainok dake kan babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

Zulum a wata takarda da ya fitar ta hannun kakakinsa, Malam Isa Gusau, ya kwatanta sojojin da suka rasa rayukansu a matsayin sadaukai wadanda suka mutu yayin kare Borno da kuma karfin ikon kasar nan.

"Ba tare da duba da abinda ya faru a Mainok ba da kuma yadda ya faru, dole ne mu yi kokarin duba sadaukantaka ta sojojin da suka rasa rayukansu yayin baiwa kasar nan kariya. Iyaye ne kuma a halin yanzu 'ya'yansu marayu ne. Matansu yanzu sun rasa mazajensu kuma iyalansu sun rasa 'yan uwa."

Asali: Legit.ng

Online view pixel