Yadda na hadu da matsafin tsoho mai shekaru 67 a yawon barbadata, Budurwa

Yadda na hadu da matsafin tsoho mai shekaru 67 a yawon barbadata, Budurwa

- Matashiyar budurwa ta yi bayanin haduwarta da tsohon matsafin da suka kwana tare

- Tace sun kwana tare amma cikin dare ya bace bayan ya saka kayan tsafi ja da baki

- Bayan ya dawo ne ya ganta tana addu'a ya bukaci ta rufe bakinta ko ta mutu gaba daya

Wata matashiyar budurwa da ta boye sunanta ta bayyana yadda tsoho mai shekaru 67 da suke soyayya dashi ya bace yayin da suke bacci.

A wani bayani dalla-dalla da tayi a kafar sada zumunta ta Facebook, matashiyar budurwar ta sanar da fastonta inda suka dinga addu'a tare da mika lamarin ga Ubangiji.

Kamar yadda cikakkiyar wallafar ta bayyana: "Na taba soyayya da wani tsoho mai shekaru 67. Ya saba bani kudi amma wata rana sai ya bukaci kwana a gidana.

KU KARANTA: Boko Haram ta raba wasika, ta sanar da dalilin kai miyagun hare-hare a Najeriya

Yadda na hadu da matsafin tsoho mai shekaru 67 a yawon barbadata, Budurwa
Yadda na hadu da matsafin tsoho mai shekaru 67 a yawon barbadata, Budurwa. Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Rashin tsaro: Ka yafewa 'yan Najeriya da suka dinga zaginka, J. Martins ga Jonathan

"Wannan mutumin matsafi ne. Yayin da zamu kwanta, sai ya bukaci in yi bacci domin washegari akwai abubuwan da zamu yi. Na yi addu'a sosai kafin in kwanta.

“Wurin karfe 2 na dare sai muka je bandaki. Na tashi amma sai na ganshi da kaya baki da ja. A take na daskare, ya lallaba zuwa wurin taga kuma ya bace.

"Na kasa ihu ko matsawa. A nan na kwashe wurin sa'a daya da rabi har ya dawo ta taga sannan ya shiga bandaki tare da dawowa kan gado.

"Mamana bacci kike? Ban ansa ba. Sai shima ya kwanta kawai. Da sassafe na sauka daga gado naje ina addu'o'i kuma tare da alkawarin ba zan sake soyayya da shi ba.

"Ya zo inda nake addu'an tare da sanar dani cewa gara in nuna ban san abinda ya faru ba, idan ba haka ba kuwa mutuwa zanyi."

A wani labari na daban, a ranar Talata, 27 ga watan Afirilun 2020, 'yan daba a jihar Sokoto sun kone ofishin 'yan sanda dake karamar hukumar Kware ta jihar.

Gungun 'yan daban da suka kunshi matasa, sun isa ofishin 'yan sandan inda suka dinga ihu tare da jaddda cewa akwai wasu wadanda aka kama da laifin garkuwa da mutane amma aka sake su.

'Yan daban sun fi karfin 'yan sandan inda suka rinjayi jami'an tsaron dake gadin ofishin kuma suka koneshi tare da motar DPO da kuma motocin sintiri guda biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng