Sunday Igboho ya sha da kyar yayin da 'yan bindiga suka kai farmaki gidansa
- Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kaiwa Sunday Igboho farmaki a gidansa
- Sun isa gidansa wurin karfe 1:30 na daren Lahadi inda suka yi musayar wuta da masu gadi
- Mai magana da yawunsa yace sun fi zargin gwamnati kuma ya bukaceta da ta kiyayi ubangidansa
Wasu 'yan bindiga da har yanzu ba a san ko su waye ba sun kaiwa Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Igboho hari a gidansa dake Soka, Ibadan a jihar Oyo.
'Yan bindigan sun kutsa gidansa kamar yadda masu magana da yawunsa, Koiki Olayomi da Dapo Salami suka sanar.
Kamar yadda suka ce, maharan sun tsinkayi gidan wurin karfe 1:30 na dare kuma sun yi yunkurin bankawa gidan wuta amma masu tsaronsa suka hana.
Duk da hadimansa basu tabbatar da cewa an yi musayar wuta ba, Vanguard ta tattaro cewa bangarorin biyu sun yi musayar wuta.
KU KARANTA: Sojoji sun kama basarake a arewa bayan samun makamai da harsasai a fadarsa
KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Mayakan Boko Haram na cikin garin Mainok dake Borno, suna ruwan wuta
Kamar yadda Koiki ya wallafa a shafinsa na Facebook, yace 'yan bindigan sun kutsa gidan Sunday dake yankin Soka na garin Ibadan a sa'o'in farko na ranar Litinin.
Wasu mazauna yankin sun ce suna sallah ne lokacin da suka ji ruwan wutan.
Duk da daya daga cikin masu magana da yawunsa yace 'yan bindigan daga gwamnati suke, babu wani takamaiman shaida da ya tabbatar da hakan.
Koiki ya ja kunnen cewa idan jami'an tsaro basu bar ubangidansa ba, wannan zai sa ya fara zama tushen matsalarsu da gwamnatin.
Koiki yace, "Yan bindigan sun iso wurin karfe 1:30 na dare. Sun yi yunkurin shiga gidan amma aka hana su. Ban san yawansu ba amma na san wasu mutane sun zo tare dasu."
A wani labari na daban, kasa da sa'o'i 24 da sheke daya daga cikin kwamandojin IPOB mai suna Ikonso a jihar Imo, 'yan ta'addan sun nada sabon shugaba.
Sakataren yada labarai na kungiyar, Emmanuel Powerful, ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da yayi da gidan talabijin na Channels a ranar Lahadi a shirin siyasa.
Powerful ya nisanta kungiyar daga zarginta da ake da kaiwa garin gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma hari. Read more:
Asali: Legit.ng