Karin Bayani: Bidiyon Ɗaliban Kaduna Da Ke Hannun Ƴan Bindiga Tsawon Kwanaki 47

Karin Bayani: Bidiyon Ɗaliban Kaduna Da Ke Hannun Ƴan Bindiga Tsawon Kwanaki 47

- 'Yan bindiga sun saki bidiyon daliban da suka sace daga kwalejin Kaduna da ke Afaka

- A cikin bidiyon, sun nuna daya daga cikin daliban mai juna biyu wacce ta roki iyayensu da su cece su

- Har wa yau, daliban sun roki gwamnatin tarayya ta cece su saboda mawuyacin halin da suka shiga na yunwa da rashin lafiya

Yan bindiga sun fitar da bidiyon daliba mai juna biyu da suka sace daga Kwallejin Nazarin Gandun Daji da ke Afaka a Jihar Kaduna.

An sace ta ne tare da sauran dalibai 38 a watan Maris na 2021.

Daily Trust ta ruwaito cewa tsakanin 5 ga watan Afirilu zuwa 8 ga watan Afrilu an sako 10 daga cikin daliban, hakan na nufin 29 na hannunsu.

Karin Bayani: Bidiyon Ɗaliban Kaduna Da Ke Hannun Ƴan Bindiga Tsawon Kwanaki 47
Karin Bayani: Bidiyon Ɗaliban Kaduna Da Ke Hannun Ƴan Bindiga Tsawon Kwanaki 47. Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Da Ɗuminsa: Ƴan IPOB Sun Yi Wa Makiyaya Fulani 19 Yankan Rago a Anambra

Da farko sun nemi a biya su Naira miliyan 500 kudin fansa amma gwamnatin Mallam Nasiru El-Rufai ta ce ba za ta bawa yan bindiga kudi ba, hakan yasa suka tuntubi wasu iyayen dalibai.

A cikin bidiyon mai tsawon mintuna hudu da dakika 56 da aka dauka cikin dare a wani wuri da ba a san ko ina bane, wani dan bindiga ya yi magana da harshen hausa sannan Fulfulde.

Ya umurci wasu daga cikin daliban su matso su yi magana cikin bidiyon.

A cikin bidiyon, matar mai juna biyu da ake cewa Hajiya ta roki iyayensu su ceto su.

"Muna kira ga iyayenmu su taimake su, mun gaji kuma babu abinci. Su yi kokari su fitar da mu daga nan. Mun shafe kwanaki 47, kusan dukkanmu bamu da lafiya kuma babu abinci. A waje muke kwana ko ana ruwan sama," in ji ta.

Ga bidiyon a kasa:

KU KARANTA: Jirgin Yaƙin NAF Ya Jefawa Motar Sojojin Ƙasa Bam Bisa Kuskure

Yan bindigan sun kuma gabatar da wata mata da aka ce matar soja ne da aka sace daga gidanta da ke Tirkania-Agwa a karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna.

Matar, wadda ta ce mijinta sojan ruwa ne da ke aiki a Warri, jihar Delta ta roki gwamnatin tarayya ta cece su.

Ta ce da farko yan bindigan sun nemi a biya Naira miliyan 30 domin a sako su.

Ku saurari karin bayani ...

A wani rahoton daban, Mallam Garba Shehu ya caccaki wadanda suke sukar Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Dr Isa Pantami saboda rashin yafe masa abin da ya yi a baya, Channels Television ta ruwaito.

Ya na ganin rashin yafewa ministan kan maganganun da ya yi na goyon bayan kungiyoyi masu tsatsauran ra'ayi ya fi muni kan laifin da ministan ya aikata.

Babban mai taimakawa shugaban kasar a bangaren watsa labarai ya yi wannan kalaman ne a lokacin da ya bayyana a shirin Politics Today na Channels Television a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel