'Yan Boko Haram Sun Zaƙewa Matan Aure a Niger Bayan Sun Musu Girki Sun Cinye
- Mayakan kungiyar ta'addanci na Boko Haram sun zakewa matan aure a Niger bayan sun musu girki
- Bulus Esu, shugaban matasa a Kuchi ya bayyana hakan yayin da Gwamna Abubakar Sani ya ziyarce su
- Gwamna Abubakar Sani shima ya tabbatar da cewa yan ta'addan sun kwace matan mutane a kauyukan suna zama da su a yanzu
Mayakan kungiyar Boko Haram sun tafka ta'adi a jihar Niger a yayin da suka ci zarafin wasu matan aure da suka basu umurnin su dafa musu abinci, Daily Trust ta ruwaito.
Bulus Esu, shugaban matasa a Kuchi, daya daga cikin garuruwan da ke yawan mutane a karamar hukumar Munya ne ya bayyana hakan yayin da Gwamna Abubakar Sani Bello ya ziyarci sansanin yan gudun hijira a ranar Litinin.
DUBA WANNAN: Karin Bayani: Bidiyon Ɗaliban Kaduna Da Ke Hannun Ƴan Bindiga Tsawon Kwanaki 47
Ese ya ce makonni biyu da suke wuce, yan ta'addan sun nemi kudin fansa har Naira miliyan 5 daga hannun mutanen garin don kada su sace su, duk da sun biya kudin, yan ta'adan sai da suka sace wasu daga cikinsu.
"Da suka sake dawowa, sun umurci matan su dafa musu abinci bayan sun dafa abincin kuma suka zakewa matan," in ji shi.
"Babu wanda ke zaune a garin Kuchi tsawon makonni uku kuma wanda suka bar garin ba su da abinci. Yan ta'addan sun ratsa garin sosai sun mamaye kauyukan. Sun mamaye Kuchi, suna kwana a can kaman gidansu."
KU KARANTA: Da Dumi-Dumi: Boko Haram Ta Kafa Tuta a Ƙauyen Jihar Niger
Gwamnan ya kuma ce yan Boko Haram din sun kwacewa wasu mutanen kauyen matansu a kan dole.
"Ina tabbatar muku cewa akwai yan Boko Haram a Kaure a karamar hukumar Shiroro a jihar Niger. Ina tabbatar muku yanzu sun kwace matar mutane sun hada su da yan Boko Haram," in ji shi.
A wani rahoton daban, Mallam Garba Shehu ya caccaki wadanda suke sukar Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Dr Isa Pantami saboda rashin yafe masa abin da ya yi a baya, Channels Television ta ruwaito.
Ya na ganin rashin yafewa ministan kan maganganun da ya yi na goyon bayan kungiyoyi masu tsatsauran ra'ayi ya fi muni kan laifin da ministan ya aikata.
Babban mai taimakawa shugaban kasar a bangaren watsa labarai ya yi wannan kalaman ne a lokacin da ya bayyana a shirin Politics Today na Channels Television a ranar Juma'a.
Asali: Legit.ng