Masu garkuwa da mutane sun sace mutane da-dama cikin daren Ramadan a Zaria

Masu garkuwa da mutane sun sace mutane da-dama cikin daren Ramadan a Zaria

- Jami’an tsaro sun cafke wasu ‘Yan bindigan da su ka kai hari a garin Zaria

- Ana zargin wadannan mutanen da aka kama, masu garkuwa da mutane ne

- Harin na zuwa ne bayan sace daliban makaranta a wata Jami’a ta Kaduna

Legit.ng Hausa ta samu labari cewa a daren da ya wuce wasu miyagun ‘yan bindiga sun shiga unguwar Kofar Gayan, Lowcost a garin Zaria, jihar Kaduna.

Kamar yadda majiyar mu ta bayyana mana, ‘yan bindigan sun yi awon-gaba da mutanen da zuwa ranar Litinin, 26 a watan Afrilu, ba a tabbatar da adadinsu ba.

Wadanda su ke zaune a wannan unguwa sun ji harbe-harben bindigogi da kimanin karshen farkon dare.

KU KARANTA: Boko Haram sun kafa tutoci a Gaidam, Yobe

A sakamakon wannan artabu da aka yi tsakanin jami’an tsaro da wadannan ‘yan bindiga, an yi nasarar kama mutum biyu da ake zargin masu satar mutane ne.

A wani bidiyo da ya shigo hannumu, za a iya jin ana murnar yin ram da wasu daga cikin wadanda su ke yin wannan danyen aiki na garkuwa da mutane.

Wani mazaunin yankin ya shaida cewa tsirarun ‘yan sandan da su ke wannan unguwa ne su ka yi ta-maza, su ka auka wa wadannan ‘yan bindiga masu yawa.

Jaridar Sahelian times ta ce ana zargin an yi gaba da wasu mutane hudu daga cikin iyalan wani Bawan Allah a unguwar da ta ke kusa da fadar Sarkin Zazzau.

KU KARANTA: Kisan Deby ya fito da rikicin cikin gidan tsohon Shugaban kasa

Masu garkuwa da mutane sun sace mutane da-dama cikin daren Ramadan a Zaria
Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai

‘Yan bindigan sun zo unguwar ne da kusan karfe 10:00 na dare. An dauki sa’a kusan uku ana ba-ta-kashi tsakanin miyagun da dakarun ‘yan sanda da ‘yan sa-kai.

Sauran wadanda su ka zo yin wannan danyen aiki sun tsere, ba su shiga hannun jami’an tsaro ba.

Kun ji cewa 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram sun yi raga-raga da mahaifar sabon shugaban hafsun 'yan sanda da tsohon Gwamnan jihar Yobe watau Giedam.

Al’umma su na kaura daga Geidam, har lamarin ya kai mutane su na barin gawar ‘Yanuwansu babu sallah, domin su tsira da ransu daga hannun 'yan ta'addan.

Duk da irin abin da yake faruwa, gwamnan jiihar Yobe, Mai Mala Buni ba ya zaune a Damaturu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel