Karin bayani: Yan ta'addan Boko Haram sun dira garin Geidam

Karin bayani: Yan ta'addan Boko Haram sun dira garin Geidam

- Sau biyu a jere, yan ISWAP sun kai mumunan hari jihar Yobe

- Da farko Sojojin sama sun samu nasarar fitittikarsu ranar Juma'a

- Hakazalika sun kai hari na'urorin kamfanonin sadarwan MTN da Airtel

Yan ta'addan Boko Haram sun kai hari karamar hukumar Geidam, mahaifar tsohon gwamnan jihar kuma Sanata mai ci a yanzu, Ibrahim Geidam.

Mazauna garin sun bayyana cewa yan bindigan sun dira garin ne da yawansu suna harbin kan mai uwa da wabi.

Bayan haka mazaunan garin Geidam a jihar Yobe sun waye gari babu daman kira mutane da wayoyinsu sakamakon katse wayoyin kamfanonin sadarwan MTN da Airtel da yan ta'addan suka yi

Garin Geidam ne mahaifar mukaddashin Sifeto Janar na yan sanda, Usman Alkali, da kuma tsohon gwamnan jihar, Ibrahim Geidam.

Da farko yan ta'addan sun kai hari garin da yammacin Juma'a, amma suka arce sakamakon ruwan wutan da Sojojin sukayi musu.

Ali Maina, daya daga cikin mazaunan garin ya ce bayan da Sojojin suka wuce, yan ta'addan suka dawo, Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce: "Sun aikata ta'asa a garin da safen nan. Muna ganin gidan na konewa kuma sun fasa shaguna suna kwashe kayen abinci."

"Abin ya fi bamu tsoro yanzu, saboda bamu san manufarsu ba. An yankemu daga layukan MTN da Airtel saboda sun yanke abin."

"Yanzu muna neman kariyan Allah ne, suna da motocin Hilux sama da 15."

Bayan haka, kakakin hukumar yan sandan jihar Yone, Dungus AnduAbdulKarim ya tabbatar da sabon harin.

DUBA NAN: Najeriya Na Bukatar N1.89trn Don Yaki da Zazzabin Cizon Sauro, Amma Babu Kudi, Minista

Karin bayani: Yan ta'addan Boko Haram sun dira garin Geidam
Karin bayani: Yan ta'addan Boko Haram sun dira garin Geidam
Asali: UGC

KU KARANTA: Munanan hare-hare, garkuwa da mutane, da kashe-kashe 6 da suka auku jiya Laraba

A bangare guda, Shugaban Hafsoshin Soji, Laftanan Janar Ibrahim Attahiru, ya bayyanawa majalisar dattawa cewa a kara musu kudi don siyan makamai da kayan yaki.

Attahiru, ya bayyana hakan ne ranar Laraba yayinda ya karbi bakuncin kwamitin majalisar dattawa kan hukumar Soji a ofishinsa dake birnin tarayya Abuja, rahoton TheCable.

Ya ce hukumar na bukatar goyon bayan kwamitin don kawar da dukkan matsalolin tsaron kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel