Da Ɗumi-Ɗumi: Ahmad Lawan ya rantsar da sabon Sanata a majalisar Dattijai
- Shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmad Lawan, ya rantsar da sabon mamba a majalisar yau, wanda aka zaɓa daga mazaɓar sanatoci dake Imo ta arewa
- An rantsar da sabon sanatan ne bayan gudanar da zaɓen maye gurbi kuma ya samu nasara a mazaɓar tasa ƙarkashin jam'iyyar APC
- Frank Ibezim, shine zai maye gurbin tsohon sanata, marigayi Benjamin Uwajumogu, wanda ya rasu a shekarar data gabata
Mamban jam'iyyar APC da aka zaɓa ya wakilci mazaɓar Imo ta arewa a majalisar dattijai ya anshi shahadar kama aiki a wajen shugaban majalisar dattijai.
KARANTA ANAN: Dalilin da Yasa Yan Arewa Zasu Fi Son Bola Tinubu Ya Zama Magajin Buhari
Shugaban sanatocin, Sanata Ahmad Lawan, ya baiwa sabon sanatan, Frank Ibezim, rantsuwar kama aikin ne a yau Talata, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Ibezim dai shine zai maye gurbin marigayi , Benjamin Uwajumogu, wanda ya rasu a shekarar data gabata
Kuma hukumar zaɓe ta gudanar da zaɓen cike gurbin kujerar tun wasu yan watanni da suka gabata.
Tun a lokacin hukumar zaɓe ta sanar da jam'iyyar APC a matsayin wacce ta lashe zaɓen, sai-dai rikicin cikin gida yasa ba'a rantsar da wanda ya samu nasarar ba.
KARANTA ANAN: Rigakafin COVID19: Wata ma'aikaciyar Lafiya ta bayyana halin da ta shiga tunda akai mata rigakafin Astrazeneca
Lamarin ya jawo kace-nace tsakanin Ifeanyi Ararume da kuma Ibezim, inda kowa ke iƙirarin shine halastaccen ɗan takara a ƙarkashin jam'iyyar APC ɗin.
Rikicin dai saida yakai gaban kotun ƙoli, wadda daga ƙarshe ta ayyana Frank Ibezim a matsayin ɗan takarar APC kuma wanda ya samu nasara a zaɓen cike gurbin da ya gabata.
A wani labarin kuma Gwamnatin Kaduna ta faɗi wani abu mai muhimmanci lokacin da taje Ta'aziyyar Ɗaliban Greenfield da aka kashe
Gwamnatin jihar Kaduna ta tura wakilai ƙarkashin jagorancin kwamishinan Ilimin jihar suje su yiwa iyayen ɗaliban jami'ar Greenfield da yan bindiga suka kashe ta'aziyya.
A jawabinsa na wajen ta'aziyyar, kwamishi nan Ilimin, Shehu Muhammed, yace gwamnati na nan akan bakarta na babu tattaunawar sulhu tsakaninta da yan bindiga.
Asali: Legit.ng