Fayose: Abinda ke faruwa da Pantami na bayyana munafincin gwamnatin Buhari

Fayose: Abinda ke faruwa da Pantami na bayyana munafincin gwamnatin Buhari

- Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya ce lamarin da ke faruwa da Pantami ya fallasa munafincin mulkin Buhari

- Ya ce abun takaici ne yadda fadar shugaban kasa ke baiwa 'yan ta'adda da ta'addanci kariya tare da aikin yi

- A cewarsa, tunda gwamnatin Buhari ta nuna cewa takardun bogi sun fi 'yan ta'adda muni, toh ba shakka ba za a samu tsaro ba

Ayodele Fayose, tsohon gwamnan jihar Ekiti, ya ce cece-kuce da ake yi a kan Isah Pantami, ministan sadarwa, ya fallasa munafincin dake kunshe a mulkin shugaba Buhari.

Wasu 'yan Najeriya da kungiyoyi sun bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya fatattaki ministan a kan tsoffin tsokacinsa a kan kungiyoyin Al-Qaeda da Taliban.

Amma a yayin martani, fadar shugaban kasa ta bakin Malam Garba Shehu, tace gwamnati tana tare da ministan, The Cable ta ruwaito.

KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun kutsa jihar Ribas, sun sheke jami'an tsaro 4

Fayose: Abinda ke faruwa da Pantami na bayyana munafincin gwamnatin Buhari
Fayose: Abinda ke faruwa da Pantami na bayyana munafincin gwamnatin Buhari. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

A wata takarda da Fayose ya fitar a ranar Lahadi, yace cece-kuce da ake yi kan Pantami ya fallasa munafincin wannan gwamnatin.

"Halin da Najeriya take ciki ta yadda yanzu fadar shugaban kasa ta zama mai bada aiki tare da kariya ga 'yan ta'addan Boko Haram da kuma 'yan bindiga, ya zama abun takaici," yace.

"Maganar Isah Pantami ta sake fallasa munafincin da bangaranci na gwamnati. Abun takaici ne da kuma tararrabi ganin cewa mai magana da yawun shugaban kasa ne yake kare shi kai tsaye."

Tsohon gwamnan yace abun bakin ciki ne yadda Najeriya ke samun shugabanci daga wani dan Boko Haram.

Yace saboda gwamnati ta kasa daukan mataki a kan 'yan ta'addan, tabbas babu batun kariya zama a kasar.

KU KARANTA: Sojoji sun kama basarake a arewa bayan samun makamai da harsasai a fadarsa

"Abun dariya ne a ce masu mulki a kasar nan ke cewa dole a kalla 'yan bindiga a matsayin marasa laifi, har sai an tabbatar da cewa suna da shi. Sun ce takardun bogi sun fi muni a kan goyon bayan 'yan ta'adda a bayyane," yace.

"Saboda sun kasa daukan mataki a kan 'yan ta'addan amma sai tausaya musu suke, hakan yasa bai dace a yi rayuwa a Najeriya ba.

" Yan ta'adda sun mamaye titunanmu yayin da 'yan Najeriya da suka hada da sarakunan gargajiya su ake sacewa har dakunan baccinsu."

Fayose ya bukaci 'yan Najeriya da su guji doguwar tafiya a kasar nan.

"Shawarata ce ga 'yan Najeriya da su zauna a mazauninsu a yanzu kuma su gujewa tafiye-tafiye a cikin kasar nan," yace.

A wani labari na daban, a halin yanzu, mayakan ta'addanci na Boko Haram suna ruwan wuta a garin Mainok dake da nisan kilomita 60 zuwa Maiduguri ta kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

Mainok ce hedkwatar karamar hukumar Kaga dake jihar Borno a arewa maso gabas na kasar nan.

Jaridar The Punch ta tattaro cewa a halin yanzu 'yan Boko Haram na bankawa gidajen jama'a wuta tare da balle shagunansu a garin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel