IPOB tayi sabon kwamanda, ta magantu a kan zarginta da kaiwa gidan Uzodinma hari

IPOB tayi sabon kwamanda, ta magantu a kan zarginta da kaiwa gidan Uzodinma hari

- Kungiyar masu rajin a raba kasar nan ta IPOB, sun nada sabon kwamanda bayan kisan Ikonso

- Kakakin kungiyar ne ya sanar da hakan a shirin siyasa da aka yi hira dashi a wata tattaunawa

- Ya sanar da cewa basu da hannu a kan kone gidan Gwamna Hope Uzodinma wanda ake zarginsu

Kasa da sa'o'i 24 da sheke daya daga cikin kwamandojin IPOB mai suna Ikonso a jihar Imo, 'yan ta'addan sun nada sabon shugaba.

Sakataren yada labarai na kungiyar, Emmanuel Powerful, ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da yayi da gidan talabijin na Channels a ranar Lahadi a shirin siyasa.

Powerful ya nisanta kungiyar daga zarginta da ake da kaiwa garin gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma hari.

Amma kuma, ya ki sanar da sunan sabon kwamandan IPOB din yayin da aka tambaye shi, The Punch ta ruwaito.

KU KARANTA: An kama miyagun ƙwayoyi cikin mutum-mutumin Maryama mahaifiyar Yesu

IPOB tayi sabon kwamanda, ta magantu a kan zarginta da kaiwa gidan Uzodinma hari
IPOB tayi sabon kwamanda, ta magantu a kan zarginta da kaiwa gidan Uzodinma hari. Hoto daga @MobilePunch
Asali: UGC

KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun kutsa jihar Ribas, sun sheke jami'an tsaro 4

"Zasu iya fadin duk abinda suke so, amma a shirye muke. An nada sabon kwamanda, amma ba zan fada sunansa ba," yace.

A dalilin da yasa aka kashe Ikonso, kakakin IPOB ya zargi cewa, "A ranar Asabar, kwamandanmu yaje kauyensu. Sun biyo shi tare da wasu 'yan siyasa kuma an umarci sojojin su kashe shi.

"An bukaci a kashe kwamandan saboda ya ki zuwa ya shugabanci sabuwar cibiyar tsaro ta Ebubeagu wacce gwamnonin kudu maso gabas suka kafa.

"Gwamnan ya tura wasu jama'a da su yi magana da kwamandan amma ya ki a kan cewa ba zai ci amanar Biafra ba da shugabannin Nazi Nnamdi Kanu. Tun daga nan, suka dinga yi masa barazana.

"A jihar Imo, sun damke mutum 50. Suna zuwa har gidaje. A Anambra, sun kwashi mutane, haka jihar Abia."

Yace babu hannunsu a harin gidan gwamna Uzodinma.

"Makaryata ne kuma ba gaskiya suke fada ba. Basu so su sanar da cewa Najeriya na tarwatsewa kuma IPOB ba za ta taba dena neman hanyar rabewa ba.

"Muna kokarin samun Biafra amma Ubangiji ne ya san lokacin. Kowa zai iya cewa komai, ba zai same mu ba," ya kara da cewa.

A wani labari na daban, dakarun sojin hadin guiwa karkashin Operation Whirl Stroke a ranar Asabar sun damke dagacin Cha (Mue Ter Cha) Utambe Adzer dake karamar hukumar Ukum ta jihar Binuwai bayan samun miyagun makamai da harsasai a fadarsa.

An gano cewa dakarun sun samu wasu makamai a fadar dagacin Lumbuv, Teran Kwaghbo a yankin kuma sun yi yunkurin kama shi amma ya tsere.

Wata majiya daga yankin da ta bukaci a boye sunanta ta sanar da Vanguard cewa dakarun OPWS sun yi aiki ne da wasu bayanan sirri inda suka gano makaman a fadar sarakunan biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel