Da duminsa: 'Yan bindiga sun kutsa jihar Ribas, sun sheke jami'an tsaro 4

Da duminsa: 'Yan bindiga sun kutsa jihar Ribas, sun sheke jami'an tsaro 4

- Jami'an tsaro hudu ne suka sheka lahira bayan 'yan bindiga sun kutsa jihar Ribas

- An gano cewa 'yan ta'addan sun halaka mutanen hudu ne a wurare mabanbanta a jihar

- Biyu daga cikinsu an halaka su ne kusa da filin sauka da tashin jiragen sama na Fatakwal

Kusan jami'an tsaro hudu ne suka rasa rayukansu bayan 'yan bindiga sun kutsa jihar Riibas a daren Asabar.

An gano cewa 'yan bindigan sun kashe jami'an tsaron a wurare daban-daban a jihar, Vanguard ta wallafa.

An gano cewa makasan sun cire kawunan mutum biyu da ake tunanin sojoji ne kusa da filin sauka da tashin jiragen sama na Fatakwal dake Omuagwa a karamar hukumar Ikwerre ta jihar Ribas.

KU KARANTA: Bidiyo: Magidanci ya bada labarin yadda ya dirkawa sirikarsa ciki, ta haifo namiji

Da duminsa: 'Yan bindiga sun kutsa jihar Ribas, sun sheke jami'an tsaro 4
Da duminsa: 'Yan bindiga sun kutsa jihar Ribas, sun sheke jami'an tsaro 4
Source: Original

KU KARANTA: Bidiyo: Magidanci ya bada labarin yadda ya dirkawa sirikarsa ciki, ta haifo namiji

Karin bayani na nan tafe...

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Kaduna ta bada wa'adin kwana bakwai kacal ga 'yan tsohuwar kasuwan Panteka dake kusa da makarantar foliteknik ta Kaduna, da su tattara komatsansu tare da barin wurin.

Kasuwar ta kasance a wurin kuma tana wanzuwa tun shekaru 60 da suka gabata. Gwamnatin ta ja kunnen 'yan kasuwan da su tattara su bar ta a cikin kwanaki 7 ko kuma su rasa kadarorinsu.

Hukumar tsari da habaka birane ta jihar Kaduna (KASUPDA), ta bada wa'adin kwana bakwai ga mazauna kasuwan fara daga ranar Juma'a da ta gabata.

Source: Legit.ng

Online view pixel