An samu sauyin lokacin jana'izar mahaifiyar Sarkin Kano

An samu sauyin lokacin jana'izar mahaifiyar Sarkin Kano

- Masarautar Kano ta sanar da daga jana'izar Hajiya Maryam Bayero zuwa ranar Litinin da safe

- A baya masarautar ta sanar da cewa za a yi jana'izar a ranar Asabar da karfe hudu na yammaci

- Mama Ode, wacce aka fi sani da Mai Babban Daki ta rasu tana da shekaru 86 a duniya

Idan Allah ya nufa, za a yi jana'izar mahaifiyar sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero da sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero, a safiyar Litinin da karfe 11.

Kamar yadda masarautar Kano ta wallafa a shafinta na Facebook, ta wallafa sanarwan sauyin lokacin jana'izar da aka samu a maimakon ranar Lahadi da aka fitar a baya.

A baya an fitar da sanarwar mutuwar Mai Babban Daki kuma za a'yi jana'izarta da karfe 4 na yammacin ranar Lahadi a Kofar Kudu ta fadar a tsakiyar birnin Dabo.

KU KARANTA: Hoton motocin alfarman miloniya Ahmed Musa masu darajar N200m sun gigita jama'a

An samu sauyin lokacin jana'izar mahaifiyar Sarkin Kano
An samu sauyin lokacin jana'izar mahaifiyar Sarkin Kano. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: El-Rufai zai rushe kasuwar Panteka, ya bada wa'adin kwana 7 ko 'yan kasuwa su rasa kadarorinsu

Marigayiya Hajiya Maryam Ado Bayero, wacce aka fi sani da Mama ko Mama Ode, ta bar gidan duniya a safiyar Asabar bayan jinyar da tayi a wani asibiti dake birnin Alkahira a kasar Masar.

Kamar yadda Sakataren masarautar Kano, Awaisu Abba Sanusi ya sanar, yace Mai Babba Daki ta rasu tana da shekaru 86 a duniya.

Marigayiyar kuma ita ce mahaifiyar Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero, kuma ita ce urwagidan tsohon Sarkin Kano, marigayi Alhaji Ado Bayero kuma ’yar sarki a masarautar Ilorin.

A wani labari na daban, jami'an hukumar 'yan sandan Najeriya da takwarorinsu na rundunar soji da farin kaya, a wani aikin hadin guiwa da suka yi a sa'o'in farko na ranar Asabar, sun tsinkayi hedkwatar 'yan ta'addan IPOB dake kauyen Awomama dake karamar hukumar Oru ta gabas a jihar Imo inda suka halaka 'yan tada kayar baya.

'Yan ta'addan ne suke da alhakin kai hari hedkwatar 'yan sandan jihar da gidan gyaran hali a ranar 5 ga watan Afirilun 2021.

Sun kai wasu jerin farmaki ga jami'an tsaro da wurare da suke a yankunan kudu maso gabas da kudu kudu na kasar nan.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel