Zaɓen 2023: Yakubu Dogara ya bayyana halin da Najeriya zata shiga idan Buhari ya sauka a 2023

Zaɓen 2023: Yakubu Dogara ya bayyana halin da Najeriya zata shiga idan Buhari ya sauka a 2023

- Tsohon shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara, yace dole sai yan Najeriya sun yi taka tsan-tsan wajen zaɓin sabbin shuwagabanninsu bayan saukar Buhari a 2023

- A cewarsa, sabida halin da ƙasar nan ta shiga ba'a buƙatar yin kuskure wajen zaɓen waɗanda basu dace a kawo ƙarshen abubuwan dake faruwa ba

- Ya ce Najeriya na buƙatar shuwagabanni da suke da ƙwarewa wajen kawo haɗin kai, zaman lafiya da kuma cigaba

Tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, yace wannan matsalar tsaron da Najeriya ke fuskanta tasa wasu sassan ƙasar nan sun fara zama abun tsoro.

Yayin da yake jawabi a wajen yaye ɗalibai karo na 10, a jami'ar Achievers dake Owo jihar Ondo, ranar Asabar, Dogara ya bayyana cewa wannan matsalar tsaron da muke ciki, an riga anyi tsammanin faruwarta tun a baya.

KARANTA ANAN: Dalilin da yasa Pantami ya tsallake binciken DSS duk da mun gano kalamansa, Tsohon Darakta yayi bayani

"Amma sai aka yi watsi da maganganun waɗanda suka yi hangen faruwar hakan, yanzun ga inda ƙasar ta tsinci kanta nan a ciki." inji Dogara

Tsohon ɗan majalisar yace a zaɓe mai zuwa na 2023, Najeriya na buƙatar mutanen dake da ƙwarewa wajen kawo haɗin kai, zaman lafiya da kuma cigaba, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Dogara yace:

"Babban ƙalubalen da yafi zama wajibi shine mu haɗa kan mutanen mu waje ɗaya, mu aje duk wani ban-banci da ya raba mu, idan kuma ba haka ba to ba zamuje ko ina ba."

"Maganar kawo cigaba a ƙasa shima abun dubawa ne, kuma yana da matuƙar muhimmanci amma bashi ne abu na farko da zamu fara fuskanta ba."

"Kada muyi kuskure, idan muka sake muka zaɓi waɗanda basu dace ba a 2023 to zamu cigaba da kasncewa a cikin baƙaƙen ranaku kamar na baya, ranakun da za'a mamaye mu, ga yunwa, yaƙi da kuma mutuwa."

Zaɓen 2023: Yakubu Dogara ya bayyana halin da Najeriya zata shiga bayan Buhari ya sauka daga Mulki a 2023
Zaɓen 2023: Yakubu Dogara ya bayyana halin da Najeriya zata shiga bayan Buhari ya sauka daga Mulki a 2023 Hoto: @yakubdogara
Asali: Twitter

KARANTA ANAN: Gwamnatin Zamfara ta haramta sayar da man fetur a wasu yankuna saboda 'yan bindiga

Ya ƙara da cewa rashin kulawar da akayi ma matasa, aka kasa samar musu da abinda ya dace, shine ya canza su daga yadda suke suka koma yan ta'adda.

"Rashin samar ma da matasa ayyukan yi domin inganta rayuwarsu, shine yasa suka canza daga ayyukan su zuwa aikin ta'addanci." Inji shi.

A wani labarin kuma Gwamnatin tarayya zata ɗauki sabbin sojoji domin ƙarfafa yaƙi da Boko Haram, Inji Ministan Tsaro

Ministan tsaro yace gwamnatin tarayya na shirye-shiryen ɗaukar sabbin sojoji waɗanda zasu taimaka wajen yaƙi da ta'addanci.

Bashir Magashi ya bayyana haka ne yayin da ya jagoranci tawagar shugabannin tsaro suka kai ziyara ga rundunar sojojin 'Operation Lafiya Dole'.

Asali: Legit.ng

Online view pixel