Shugaba Buhari ya yi Allah-wadai da kisan daliban jami'ar Greenfield 3 a Kaduna

Shugaba Buhari ya yi Allah-wadai da kisan daliban jami'ar Greenfield 3 a Kaduna

- Shugaba Buhari yayi tsokaci kan kisa da garkuwa da dalibai a jami'ar Greenfield

- Buhari ya alhinin abin da ya faru kuma ya jajantawa iyalan mamatan

- Ya lashi takobin cewa zai kawo karshen matsalar tsaron da kasar nan ke fama da ita

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da kisan daliban jami'ar Greenfield da aka sace kwanaki 3 da suka gabata a makarantarsu dake jihar Kaduna.

Buhari ya bayyana cewa wannan hare-hare da kashe-kashen da ake yi a jihar Kaduna abin takaici ne.

A jawabin da ya saki da ranar Asabar a Tuwita, ya lashi takobin cewa sai gwamnatinsa ta kawo karshen wadannan yan bindigan da dukkan dukiyar da kasar nan ta mallaka.

"Kisan dalibai uku cikin wadanda aka sace a jami'ar Greenfield Kaduna, abin takaici ne kuma ina Allah-wadai," Buhari yace.

"Ina mai jajantawa iyalansu kuma Allah ya jikansu."

"Wannan hare-hare da kashe-kashen dake faruwa, musamman a jihar Kaduna, abin takaici ne. Muna tabbatar da cewa zamu cigaba da yaki da dukkan yan bindiga, masu garkuwa da mutane da duk dukiyar da kasar nan ta mallaka."

DUBA NAN: Munanan hare-hare, garkuwa da mutane, da kashe-kashe 6 da suka auku jiya Laraba

Shugaba Buhari ya yi Allah-wadai da kisan daliban jami'ar Greenfield 3 a Kaduna
Shugaba Buhari ya yi Allah-wadai da kisan daliban jami'ar Greenfield 3 a Kaduna
Asali: UGC

DUBA NAN: Sai kun kara mana kudi zamu iya kawar da yan ta'adda, Shugaban Hafsan Soji Attahiru

Kun ji cewa yan bindigan da suka kai hari jami’ar GreenField dake Kaduna inda sukayi awon gaba da dimbin dalibai sun bindige mutum 3 cikin daliban da suka sace.

Hakan na kunshe cikin jawabin da Kwamishanan tsaro da harkokin cikin gidan Kaduna, Samuel Aruwan, ya saki ranar Juma’a.

An tsinci gawawwakin daliban uku ranar Juma’a a kauyen Kwanan Bature, dake kusa da jami’ar, Aruwan ya kara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel