‘Muna da Ƙarfin Murƙushe Ku’, Buhari Ya Gargaɗi Ƴan Bindiga Kan Kisar Mutum 83 a Zamfara
- Shugaba Muhammadu Buhari ya gargadi ƴan bindiga akan kisar mutane da dama a Zamfara
- Shugaban ƙasar ya ce gwamnatinsa tana da ƙarfin da za ta iya murƙushe ƴan bindigan
- Buhari ya umurci hukumomin tsaro su zage damtse domin taka wa ɓata garin birki
Shugaba Muhammadu Buhari ya gargadi ƴan bindiga cewa gwamnatinsa na da ƙarfin murƙushe su, The Cable ta ruwaito.
Buhari ya yi wannan gargaɗin ne sakamakon kashe mutane da dama da ƴan bindiga suka yi a garuruwan Zamfara.
DUBA WANNAN: Sunayen sabbin alƙalai 18 da Buhari ya amince da naɗinsu a kotun daukaka ƙara
Rahotanni sun nuna cewa an kashe fiye da mutum 25 a harin da aka kai a ƙananan hukumomin Gobirawa, Rini, Gora, Madoti Dankule, Bakura da Maradun a Zamfara - tuni dai adadin waɗanda aka kashe ya ƙaru.
Ƴan bindigan sun afka garuruwan a kan babur suka rika harbe-harbe a ranar Laraba.
Da ya ke martani kan batun, Buhari ya ce "dole a dakatar da kisar da aka yi wa mutanen da basu jiba ba su gani ba," ya ƙara da cewa dole a kawo karshen abin."
"Kada waɗannan ɓata-garin su yi tunanin cewa gwamnati ba za ta iya murƙushe su bane," kakakin shugaban ƙasa Garba Shehu ya ruwaito shugaban kasar ya faɗa a ranar Alhamis.
KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Fursunoni sunyi yunƙurin tserewa daga gidan yari a Kano
Ya ce gwamnatinsa ba za ta amince da rika cin zalin mazauna ƙauyuka da ke fama da talauci da ƙallubalen rayuwa.
Shugaban ƙasar ya umurci hukumomin tsaro su zage damtse domin ganin sun taka wa ɓata garin birki.
Buhari ya bawa mazauna jihar tabbacin cewa gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa domin cin galaba kan maƙiya duk da wannan koma bayan da aka samu.
Asali: Legit.ng