NCC ta kama wasu mutane biyar da zargin rijista da kuma saida layin waya ba bisa ƙa'ida ba

NCC ta kama wasu mutane biyar da zargin rijista da kuma saida layin waya ba bisa ƙa'ida ba

- NCC ta sanar da kama mutane biyar waɗanda take zargi da aikata laifin rijistar layin waya ba bisa ƙa'ida ba a Abuja

- Hukumar ta samu wannan nasara ne tare da haɗin gwuiwar jami'an tsaron DSS, da kuma na hukumar NSCDC

- NCC tace wannan somin taɓi ne, za'a cigaba da gudanar da wannan aikin a sauran jihohin ƙasar nan

Hukumar dake kula da kamfanonin sadarwa NCC ta sanar da kama wasu mutane biyar da zargin yin rijistar layin waya ba bisa ƙa'ida ba da kuma siyar dashi.

NCC tace an kama mutanen ne a wani aikin haɗin gwuiwa tsakanin sashin saka idanu na NCC, DSS, da kuma jami'an tsaro na NSCDC a unguwar Wuse, Abuja.

KARANTA ANAN: Yan Sanda sun damƙe mutane huɗu da zargin kashe wani Sabon ango kwana ƙaɗan kafin bikinsa

Hukumar NCC ta bayyana hakane a wani jawabi da ta fitar a Abuja ranar Alhamis ta bakin Daraktan yaɗa labaranta, Ikechukwu Adinde.

A jawabin yace:

"An miƙa waɗanda aka kama ɗin ga hukumar NSCDC reshen Abuja, domin su ƙara gudanar da bincike kan zargin da ake musu."

Shugaban sashin ayyuka na NCC, Salisu Abdu, wanda ya jagoranci tawagar haɗin gwuiwar, yace wannan aikin na daga cikin ayyukan da hukumar ta fara na yau da kullum domin daƙile masu laifi waɗanda ake haɗa hannu dasu wajen yin rijistar layi ba bisa ƙa'ida ba.

NCC ta kama wasu mutane biyar da zargin rijista da kuma saida layin waya ba bisa ƙa'ida ba
NCC ta kama wasu mutane biyar da zargin rijista da kuma saida layin waya ba bisa ƙa'ida ba Hoto: technext.ng
Asali: UGC

KARANTA ANAN: Bincike: Mafi yawancin Gwamnonin dake kan madafun iko sun fito ne daga wannan jami'ar

Salisu yace: "Yin rijistar layi ba tare da ɗaukar bayanan wanda zaiyi amfani dashi ba babban laifine da ake hukunci kansa ƙarƙashin dokokin kamfanonin sadarwa, hakanan laifine a ƙarƙashin dokokin ƙasa."

"Duk da gwamnatin tarayya ta ɗage dokar hana yin rijistar sabon layi, ya zama wajibi muyi rijistar sabon layin waya yadda yakamata, kuma mu haɗa shi da lambar katin ɗan ƙasa (NIN)."

Salisu Abdu ya gargaɗi duk wanda yasan yana makamancin irin wannan laifin da ya gaggauta bari tun kafin NCC ta iso gareshi.

Ya kuma tabbatar da cewa wannan aikin zai cigaba a Abuja da sauran jihohin ƙasar nan kamar yadda Punch ta ruwaito.

A wani labarin kuma Mazauna Kano sun koka da tashin gwauron zabi da farashin ƙanƙara yayi a watan Azumi

Mazauna garin Kano sun koka matuƙa da tashin gwauron zabi da farashin ƙanƙara yayi duk kuwa da shigowar watan Azumin Ramadan.

Mutane da yawa sunce farashin ƙanƙarar ya ƙaru sama da kashi 100%, domin ƙanƙarar da ake siyarwa N100 kafin azumi yanzun ta koma N250.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: