Mai shekaru 55 ta haifi santala-santalan yara har uku bayan tsawon jira na shekaru
- Bayan jira na tsawon shekaru, wata mata mai shekaru 55 ta haifi yara har uku lafiyayyu
- Ta bayyana cewa, da farko bata yarda cikin da take dauke dashi na gaske bane har sai da ta haihu
- Ta kuma nuna godiya ga Allah da ya bata irin wannan kyauta da ba a ko ina take samuwa ba
Wata mata mai shekaru 55, mai suna Misis Tegbe Awusaziba, daga garin Otuokpoti da ke karamar Hukumar Ogbia a Jihar Bayelsa, ta haifi ’yan uku bayan ta yi shekaru da yawa ba tare da ta haihu ba.
Da ake ba da labarin yadda abin al'ajabin ya faru, an ce Mrs Awusaziba ta haihu ne ta hanyar tiyatar haihuwa a asibiti, Daily Trust ta ruwaito.
Dukkan al’ummar Otuokpoti sun je taya ta murna lokacin da suka sami labarin haihuwar Misis Awusaziba.
KU KARANTA: Majalisar Dattawa na duba yiyuwar hanyar sanin yawan shanu da awakai a Najeriya
An ruwaito cewa dukkan jariran da aka haifa da mahaifiyarsu suna cikin cikakken koshin lafiya.
Da take magana, Misis Awusaziba ta ce ba ta yarda da cewa ciki na gaske take dauke dashi ba a farkon lokacin da ta samu ciki saboda shekarunta, kuma ta nuna godiya ga Allah.
KU KARANTA: Manhajar albashin jihar Bauchi ta lalace, an dakatar da albashin wasu ma'aikata
A wani labarin, Mutanen kabilar Yaohnanen da ke tsibirin Vanuata wadanda ke bauta wa Yarima Philip a matsayin allansu sun ce sun yi imanin cewa ruhinsa zai dawo gida garesu a tsibirinsu.
A cewar mutanen, marigayi Duke na Edinburgh zai kawo zaman lafiya da jituwa a duniya, Daily Mail ta ruwaito.
Wani daga cikin 'yan kabilar ya ce duk wani farin ciki daga gare shi yake, yayin da wani ya ce yana matukar kaunarsa kuma yana addu'ar cewa rayuwarsa ta hadu da ta Yarima Philip.
Asali: Legit.ng