Pantami ne babban limamin ATBU lokacin da musulmi suka kashe ɗa na a masallaci, Farfesa

Pantami ne babban limamin ATBU lokacin da musulmi suka kashe ɗa na a masallaci, Farfesa

- Farfesa Samuel Achi, tsohon malami a jami'ar Kaduna ya bayyana yadda musulmi suka kashe dansa, Sunday, a jami'ar ATBU a lokacin Pantami ne babban limami

- Achi ya ce abin ya faru ne a watan Disambar 2004 inda aka zargi dansa da yada wata takarda mai dauke da batanci kuma aka fitar da fatwa akansa aka kashe shi

- Farfesan wanda ya musanta cewa akwai batanci cikin takardan da dansa ya yada ya ce idan da Pantami mutum ne mai son zaman lafiya da ba a kashe dansa ba

- Hadimar Pantami, Uwa Sulaiman, ta musanta zargin da Farfesa Achi ya yi duk da cewa ba ta yi karin haske ba a kan lamarin

Farfesa Samuel Achi, tsohon malami a Jami'ar jihar Kaduna ya bayyana yadda aka kashe dansa, Sunday, a masallacin Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa, ATBU, da ke Bauchi a lokacin da Ministan Sadarwa da Tattalin arzikin zamani, Isa Pantami, ne babban limamin masallacin jami'ar.

Tsohon lakcaran ya ce shaƙe dansa aka yi a masallacin jami'ar ta ATBU saboda ya raba wata takarda da ke dauke da sakon da aka ce batanci ne ga addinin musulunci a ranar 9 ga watan Disambar 2004.

Pantami limami ne a ATBU a lokacin da musulmi suka yi fatawa, suka kashe da na a masallaci, Farfesa
Pantami limami ne a ATBU a lokacin da musulmi suka yi fatawa, suka kashe da na a masallaci, Farfesa. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

A hirar da ya yi da The Punch a ranar Laraba, ya ce dansa mai shekaru 24 yana aji na 4 ne a jami'ar a lokacin kuma shine shugaban kungiyar dalibai kirista ta Evangelical Church Winning All Ministry a lokacin.

Farfesan ya ce takardar da dansa Sunday ya raba bata dauke da batanci amma duk da haka al'ummar musulmi da ke jami'ar karkashin jagorancin Pantami sun fitar da fatwa da ta yi sanadin kashe dansa.

DUBA WANNAN: Maigida ta nemi na kwanta da ita a madadin biyan kuɗin haya, in ji Saurayi

Ya ce sai da ya nemi taimakon gwamnonin jihohin Kaduna da Bauchi na wannan lokacin kafin ya samu gawar dansa Sunday domin a birne shi.

Mahaifin marigayi Sunday ya ce, "Abin ya faru ne a safiyar ranar 9 ga watan Disambar 2004. Daga daren ranar 8 ga watan Disamba ne zuwa awannin farkon ranar 9 ga watan Disamba ya faru. Binciken da na yi ya nuna ba jefe shi aka yi ba. Shake shi aka yi a cikin masallaci. An gano gawarsa a wajen masallacin jami'ar."

Malamin jami'ar ya ce ya yafe wa dukkan wadanda ke da hannu wurin kashe dansa amma ya jadada cewa idan da Pantami wanda shine babban limamin jami'ar a lokacin mutum ne mai son zaman lafiya, da dansa bai mutu ba.

Wani babban jami'i a ATBU da ya nemi a sakaya sunansa shima ya tabbatarwa The Punch cewa an kashe Sunday ne a Disambar 2004 a lokacin Pantami ne babban limamin masallacin jami'ar.

Sai dai, hadimar Pantami, Uwa Suleiman ta shaidawa majiyar Legit.ng cewa ikirarin da Farfesan ya yi ba gaskiya bane. Ba ta yi karin bayani kan batun ba.

KU KARANTA: Kotun shari'a ta raba aure a Zamfara saboda tsabar girman mazakutar miji

Hadimar ministan ta ce, "Zargin ba gaskiya bane. Ka tafi ka yi bincike da kanka amma zargin ba gaskiya bane."

A cikin yan kwanakin nan wasu na yi wa Pantami matsin lamba ya yi murabus daga mukaminsa saboda wasu maganganu da ya yi a kan kungiyoyin ta'addanci da suka hada da Taliban da Al-Qaeda.

A bangarensa, Pantami ya ce ra'ayinsa ya sauya kan batun inda ya ce kuruciya ne a lokacin ta dibe shi amma ya zurfafa bincike kuma ya sauya ra'ayinsa.

A wani labarin daban kun ji cewa 'yan sanda a jihar Kano sun ceto wata yarinya mai shekaru 15, Aisha Jibrin, da iyayenta suka kulle ta a daki tsawon shekaru 10 a Darerewa Quaters a karamar hukumar Fagge ta jihar Kano.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata ya ce mahaifiyarta Rabi Muhammad tana hannunsu amma mahaifinta ya tsere.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata ya ce mahaifiyarta Rabi Muhammad tana hannunsu amma mahaifinta ya tsere.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel