Wani mutum ya kashe maƙwabcinsa ana sauran kwana 6 aurensa
- Wani mutum ya hada baki da abokansa ya halaka makwabcinsa daf da aurensa a jihar Kwara
- Bayan halaka makwabcin, sun kuma sace Naira miliyan 1.2 daga asusun bankinsa sannan suka nemi iyalansa su biya kudin fansa
- Kakakin rundunar yan sandan jihar Kwara, Ayayi Okasanmi ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce sun kama wasu a halin yanzu
Wani ma'aikatan Hukumar Inshorar Lafiya na Kasa, NHIS, a asibitin koyarwa na Jami'ar Ilorin, Olokose Oluwasola Ojo ya gamu da ajalinsa kwanaki shida kafin aurensa, Daily Trust ta ruwaito.
Makwabcinsa mai suna Mohammed tare da abokansa ne suka halaka Ojo mai shekaru 30 da yan kai saboda suyi tsafi da shi.
Wadanda ake zargi matsafa ne sun yi gunduwa-gunduwa da jikinsa sun cire wasu sassa sannan suka saka a cikin buhu kamar yadda yan sanda suka gano sannan suka kai gawar asibitin UITH.
DUBA WANNAN: Sheikh MaiAnnabi: Iyalan malamin Kano sun shiga fargaba yayinda wa'adin da masu garkuwa suka basu ya kusa cika
An kuma gano cewa wadanda ake zargin sun watsa wa gawarsa acid saboda kada ta yi wari a unguwar.
Yan uwansa sun tafi asibitin na UITH a ranar Talata sun karbi gawarsa domin a tafi da shi garinsu a jihar Ondo a yi masa jana'iza.
Wanda abin ya faru da shi ya bawa wanda ake zargin N350,000 domin ya siyo masa shanu uku da za a yi amfani da su yayin auren amma shi da tawagarsa suka tare shi a hanyar Patigi suka kashe shi.
DUBA WANNAN: An yi tonon asiri tsakanin sojoji da wasu fararen hula kan taimakon ƴan Boko Haram
Maharan sun kwace katin ATM dinsa sun cire Naira miliyan 1.2 daga asusun bakinsa sannan daga bisani suka nemi iyalansa su biya Naira miliyan 12 kudin fansa.
Kakakin yan sandan jihar Kwara, Ajayi Okasanmi ya ce, "Mun fara bincike a kan lamarin sannan mun kama wasu mutane, abin da kawai zan iya cewa a yanzu kenan."
A wani labarin daban kun ji cewa 'yan sanda a jihar Kano sun ceto wata yarinya mai shekaru 15, Aisha Jibrin, da iyayenta suka kulle ta a daki tsawon shekaru 10 a Darerewa Quaters a karamar hukumar Fagge ta jihar Kano.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata ya ce mahaifiyarta Rabi Muhammad tana hannunsu amma mahaifinta ya tsere.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata ya ce mahaifiyarta Rabi Muhammad tana hannunsu amma mahaifinta ya tsere.
Asali: Legit.ng