Yanzu-yanzu: Bayan nasara a zabe, Shugaban kasar Chadi, Idris Deby, ya mutu

Yanzu-yanzu: Bayan nasara a zabe, Shugaban kasar Chadi, Idris Deby, ya mutu

- Duniya juyi-juyi, shugaban kasa ya mutu a faggen daga

- Yan tawaye sun budewa shugaban kasan wuta ne a artabun da suka yi

- Deby ya mulki kasar Chadi na tsawon shekaru 30, tun 1990

Labarin da ke shigo mana da duminsa daga AFP na nuna cewa shugaban kasar Chadi, Idris Deby, ya riga mu gidan gaskiya, bayan samun nasara a zaben kasar.

Rahotanni sun nuna cewa Idris Deby ya mutu ne sakamakon harbin da akayi masa a faggen yaki da yan tawaye.

An saki sakamakon nasararsa a zaben ne ranar Litnin.

Idris Deby ya mutu yana mai shekaru 68.

Ya hau mulkin kasar bayan tawaye a shekarar 1990. Ya lashe kashi 79.3% na zaben da aka gudanar ranar 11 ga Afrilu.

Ya kwashe shekaru 30 yana mulki.

KU KARANTA: Ba za'a kara farashin man fetur ba a watan Mayu, Shugaban NNPC

Yanzu-yanzu: Bayan nasara a zabe, Shugaban kasar Chadi, Idris Deby, ya mutu
Yanzu-yanzu: Bayan nasara a zabe, Shugaban kasar Chadi, Idris Deby, ya mutu

KU DUBA NAN: Milyan 17 muka biya don a sake mana 'yayanmu 39 amma 10 aka saki, Iyayen daliban Kaduna

Yan tawayen FACT sun kai hari iyakan kasar dake Tsibetsi a ranar 11 ga Afrilu, ranar da aka fara zaben shugaban kasa.

Hukumar Sojin bata bayyana takamammen ranan da Deby ya mutu ba. Hakazalika basu bayyana kwanakin da ya kwashe yana jinya ba.

Da farko hukumar Sojin ta sanar da cewa ta samu nasara kan yan tawayen. Amma bidiyon Aljazeera ya nuna lokacin da aka dawo da shugaban kasan a hannu ya samu raunuka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel