An Kama fursunoni tara cikin waɗanda suka gudu daga gidan yarin Owerri a kasar Ghana

An Kama fursunoni tara cikin waɗanda suka gudu daga gidan yarin Owerri a kasar Ghana

- Hukumar yan sandan ƙasar Ghana ta kama tara daga cikin fursunonin da suka gudu daga gidan yari a Najeriya

- Yan sandan sun ce sun kama waɗanda ake zargin ne bayan samun bayanai akansu, kuma suka ɗana musu tarko

- A kwanakin baya dai ,fursunoni sama da 1,800 ne suka gudu daga gidan yarin Owerri, jihar Imo a lokacin da wasu yan Bindiga suka kai hari

Hukumar yan sanda a ƙasar Ghana ta kama fursunoni tara da suka gudu daga Najeriya suka shiga ƙasar kamar yadda jaridar Dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Sheikh Pantami ya bayyana wata babbar Nasara da gwamnatin tarayya ta samu a ɓangaren Fasahar Zamani

An kama fursunonin ne mako ɗaya bayan ɓalle gidan yarin Owerri dake jihar Imo da wasu yan bindiga suka yi.

Sama da yan fursuna 1,800 ne suka fice daga gidan bayan yan bindigar sun mamaye gidan yarin a ranar biyar ga watan Afrilu.

A jawabin shugaban ofishin yan sanda dake Ada, Francis Somian, yace an kama fursunonin ne bayan samun cikakken bayani akan su.

Jami'an yan sandan sun bayyana cewa waɗanda ake zargin sun amince da cewa sun gudu ne daga gidan yari a Najeriya suka shigo ƙasar Ghana ta jirgin ruwa.

Rahotanni sun tabbatar da cewa fursunonin sun ƙetare kogin Volta, suka shiga Ada Foah, inda suka yi ƙoƙarin cigaba da tafiya zuwa Accra, babban birnin ƙasar Ghana.

An Kamo fursunoni tara a Ghana waɗanda suka gudu daga gidan Yari lokacin harin yan bindiga
An Kamo fursunoni tara a Ghana waɗanda suka gudu daga gidan Yari lokacin harin yan bindiga Hoto: @correctionsNG
Asali: Twitter

KARANTA ANAN: EFCC ta kowa ce, Babu wanda ya isa ya juya ta, inji Abdulrasheed Bawa

Waɗanda aka kama ɗin sun haɗa da; Emmanuel Obinnah Chiedozie, Steve Eyenuku, Enebeli Lucky, Yommi Usmah, Keli Ekureni, Freedom Yusuf, Obi Onuora, Patrick Chanar, da kuma Bless Eyenuku.

A lokacin da aka kama waɗanda ake zargin, an samu kuɗin Najeriya da na Ghana a tare dasu, kayayyakin sawa, fasfot, da kuma katin shaida (ID).

Hukumar gyaran hali ta Najeriya ta fitar da bayanan wasu daga cikin fursunonin da suka gudu yayin harin.

Sai-dai gwamnatin Najeriya tayi alƙawarin yafewa duk wani fursuna da ya dawo don ƙashin kansa.

A wani labarin kuma Rundunar Yan sanda ta Kuɓutar da yara ƙanana 19 da wasu mata 6 da ake ƙoƙarin safararsu

Rundunar yan sanda reshen jihar Edo ta kuɓutar da mutane 26 a jihar waɗanda akayi kokarin safarar su

Hukumar tace waɗanda ta kuɓutar ɗin sun haɗa da ƙananan yara 19, da kuma matashiya ɗaya, sai kuma iyaye mata su shida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262