Watan Ramadan: Gwamnatin Zamfara ta kashe 2.9 Biliyan wajen Tallafa ma talakawa a watan Ramadan

Watan Ramadan: Gwamnatin Zamfara ta kashe 2.9 Biliyan wajen Tallafa ma talakawa a watan Ramadan

- Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana cewa ta kashe kuɗaɗe kimanin Biliyan N2.9bn wajen siyo kayan abinci da rabasu ga talakawan jihar

- Kwamishinan yaɗa labaran jihar ne ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar a Gusau, babban birnin jihar ranar Lahadi

- Daga cikin kayyayakin abincin da gwamnatin ta siyo ta raba akwai; buhunan shinkafa, Gero, wake, Masara, da kuma na Sukari

Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana cewa ta kashe kimanin 2.9 biliyan wajen siyo kayayyakin amfani domin rabawa talakawan jihar a wannan wata da muke ciki na Ramadana.

Kwamishinan yaɗa labaran jihar, Ibrahim Dosara, shine ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar a Gusau, babban birnin jihar ranar Lahadi.

KARANTA ANAN: Yadda Mutum 20 suka mutu a hare-haren ramuwar gayya tsakanin Yan Bindiga da Jami'an Bijilanti

Kwamishinan yace shugaban kwamitin raba kayan tallafin na wannan shekarar, wanda kuma shine kakakin majalisar dokokin jihar, Nasiru Magarya, ya tabbatar da cewa kayayyakin zasu kai ga talakawan da akayi domin su.

Ya kuma ƙara da cewa, kakakin majalisar ya ƙara naɗa kwamitoci domin samun sauki wajen rabon tallafin kamar yadda Punch ta ruwaito.

Dosara ya ƙara bayyana cewa an samar da manyan motocin ɗaukar kaya 450 ɗauke da kayayyakin walwala da jin dadi.

Daga cikin kayayyakin da motocin ke ɗauke dasu akwai: Shinkafa, Gero, Masara, Wake, Sikari, da kuma madara.

Watan Ramadan: Gwamnatin Zamfara ta kashe 2.9 Biliyan wajen Tallafa ma talakawa a watan Ramadan
Watan Ramadan: Gwamnatin Zamfara ta kashe 2.9 Biliyan wajen Tallafa ma talakawa a watan Ramadan Hoto: @Zamfara_state
Asali: Twitter

An kuma raba dukkan su ga mutane marasa ƙarfi, talakawa, waɗanda aka raba su da mahallansu, ma'aikata da sauran su.

KARANTA ANAN: PDP ta sake huro ma Pantami wuta, ta yi kira ga DSS ta gayyaci Ministan ya amsa tambayoyi

"Maƙasudin bada wannan tallafi shine don a rage wahalar rayuwa da mutane ke fama da ita, kuma su samu damar gudanar da azumin ramadana cikin sauƙi da kuma farin ciki." inji Dosara.

Hukumar dillancin labarai ta Najeriya NAN ta ruwaito cewa kayan da aka raba ɗin sun haɗa da; Buhunan shinkafa 60,000, Gero buhu 50,000, buhunan masara 50,000, Wake buhu 30,000, Sikari buhu 10,000 da kuma katan-katan ɗin madara.

A wani labarin kuma Gwamnatin tarayya zata ɗauki sabbin sojoji domin ƙarfafa yaƙi da Boko Haram, Ministan Tsaro

Ministan tsaro yace gwamnatin tarayya na shirye-shiryen ɗaukar sabbin sojoji waɗanda zasu taimaka wajen yaƙi da ta'addanci.

Bashir Magashi ya bayyana haka ne yayin da ya jagoranci tawagar shugabannin tsaro suka kai ziyara ga rundunar sojojin 'Operation Lafiya Dole'.

Asali: Legit.ng

Online view pixel