A wurin liyafa, ango ya zabgawa amarya mugun mari, 'yan biki sun sha mamaki

A wurin liyafa, ango ya zabgawa amarya mugun mari, 'yan biki sun sha mamaki

- Wata ma'abociyar amfani da kafar sada zumuntar Twitter ta bada labarin yadda ango ya zabgawa amarya mari a wurin bikinsu

- Amma kuma abun takaicin shine yadda iyaye, 'yan uwa da abokan arziki ke kallon abinda ya faru ba tare da sun ce komai ba

- Daga bisani, amaryar ta ja hannun angon tare da ce mishi su shiga wurin liyafar domin bakinsu suna ta jiransu

Wata ma'abociyar amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Twitter ta bada labarin yadda ta shiga mamaki bayan ango ya zabgawa amarya mari a wurin liyafar bikinsu.

@MmantiUmoh wacce tace babu soyayya tsakaninta da mutane masu hargitsi, ta ce lamarin ya faru ne yayin da angon ya zabgawa amarya mari a gaban iyaye tare da sauran 'yan gida. Ta ce hakan yasa ta ji bata da ra'ayin zuwa bukukuwa.

Kamar yadda tace: "A wurin liyafa ango ya mari amarya wanda karfin marin yasa muka yi tunanin ko balan-balan ce ta fashe. Yayin da muka dauki dakika 10 kafin mu watsake daga firgicin, sai muka ji tana cewa "Rabin raina mu shiga ciki, na gaji da tsayuwa kuma ana ta maganganu. Mu shiga a fara shagali, kowa mu yake jira."

A wurin liyafa, ango ya zabgawa amarya mugun mari, 'yan biki sun sha mamaki
A wurin liyafa, ango ya zabgawa amarya mugun mari, 'yan biki sun sha mamaki. Hoto daga @MmantiUmoh
Asali: Twitter

KU KARANTA: Miji ya kone duk takardun kammala makarantun matarsa bayan fada ya hada su

KU KARANTA: Dukkan biliyoyin da na tara sun kasa samar min da farinciki, Biloniya Otedola

"Abu daya da dolenka ga mutane shine ka mutunta su. Amma bai zama dole kayi hakuri da fushinsu ba. Ba dole ka nunawa fitinannun mutane soyayya ba. Har abada, babu soyayya."

Kamar yadda tace, hatta babban abokin angon tambayar amaryar yake yi "Me kika yi mishi, mai yasa ranshi ya baci?"

Amma kuma ana sakin waka, kowa ya koma cikin shagalin inda aka dinga rawa tare da cashewa.

Kamar yadda ta kara da cewa, iyayensu sun ga lokacin da aka yi marin, hakazalika wasu 'yan uwansu. A take ta juya ta koma gida tana fama da ciwon kai. Ta kara da cewa ta dena zuwa bukukuwa na dan wani lokaci, sai dai ta aika gudumawa.

A wani labari na daban, tsohon shugaban kasan Najeriya, Goodluck Jonathan, ya ce Babangida Aliyu, tsohon gwamnan jihar Neja yayi karya da yace gwamnonin PDP na arewacin Najeriya sune suka kayar dashi a 2015 ta hanyar hade masa kai.

A ranar Juma'a, Aliyu yace gwamnonin PDP na jihohin arewacin Najeriya sun soki bukatarsa ta zarcewa bayan ya ki cika alkawarinsa na hakura da mulki a wa'adin farko.

"Tunda hakan ya ci karo da yarjejeniyarmu ta farko a jam'iyyar, kuma mu gwamnonin arewa muke ganin za a cuce mu idan Jonathan yayi nasara, sai muka tashi muka hana hakan faruwa," yace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng