Masu garkuwa da mutane sun sa N20m a kan wuyan Sarkin da su ka yi awon-gaba da shi

Masu garkuwa da mutane sun sa N20m a kan wuyan Sarkin da su ka yi awon-gaba da shi

- Wadanda su ka sace Sarkin Oye sun bukaci a biya fansar Naira miliyan 20

- Masu garkuwa da mutanen sun tuntubi iyalin mai martaba a makon jiya

- Jami’an tsaro sun ce su na bakin kokarinsu na ganin Sarkin ya dawo gida

Iyalin Sarki Obadu na kasar Ilemeso Ekiti da ke karamar hukumar Oye, jihar Ekiti, sun shiga wani mawuyacin hali a sakamakon sace mai martaba da aka yi.

Jaridar Punch ta bayyana cewa tun da masu garkuwa da mutane su ka dauke Basaraken a ranar Alhamis, har yanzu ba a iya nasarar kubutar da shi ba.

Manema labarai sun zanta da iyalin mai martaban inda su ka bayyana cewa ‘yan bindigan sun tuntube su a ranar Asabar, kuma sun sa masu kudin fansa.

Kara karanta wannan

Matar Aure Ta Bayyana Yadda Kidinafas Suka Bata N2,000 Bayan Karbar N6m daga Mijinta

KU KARANTA: 'Yan sanda sun cafke Basaraken da ke taimakawa 'Yan bindiga

Kamar yadda ‘yanuwan Mai martaba, Oba Oyewumi, su ka bayyana, masu garkuwa da mutanen sun bukaci su biya Naira miliyan 20 kafin a fito da shi.

Majiyar ta ce: “Masu garkuwa da mutanen sun tuntubi danginsa da kimanin karfe 7:00 a ranar Asabar, su ka bukaci mu biya N20m kafin a fito da Sarkin.”

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Sun kira wayar ne da layin Kabiyesi (Mai martaba), tun lokacin kuma wayarsa ta ke a kashe.”

“Mun damu sosai da bukatun da aka lafta. Mun kagara Mai martaba ya dawo mana cikin koshin lafiya. Iyalinsa na kokarin ganin an yi maza an fito da shi.”

Masu garkuwa da mutane sun sa N20m a kan wuyan Sarkin da su ka yi awon-gaba da shi
Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi

KU KARANTA: Kudin da ke shiga lalitar mu ya ragu, bukatar kudi ya karu - Minista

Kara karanta wannan

Kamfen 2023: 'Yan A Mutun APC Na Bin Gida-gida Don Tallata Dan Takararsu Bola Tinubu A Wata Jahar Arewa

Da aka tuntubi ‘yan sanda, babban jami’in hulda da jama’a na rundunar jihar Ekiti, Sunday Abutu, ya bayyana kokarin da su ke yi na ganin sun ceto Sarkin.

“Mu na bin duk matakan da za a iya na tsaro domin ganin mun kubuto da Sarkin. Ba mu zauna ba.”

Abutu ya ce: “Mu na aiki da sauran takwarorinmu a kan wannan lamari, kuma mu na tattara bayanan da mu ka samu. Mu na aiki ne da ingantattun bayanai.”

Kwanakin baya kun samu rahoto Gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu ya sa hannu a kan wasu sababbin dokokib da za su magance manyan laifuffuka a jiharsa.

Sanata Atiku Bagudu ya amince da hukuncin kisa ga duk wanda aka samu da laifin garkuwa da mutane, sannan za a zartar da daurin rai da rai a kan masu fyade.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng