Garkuwa da mutane: 'Yan sanda sun cafke wani basarake a jihar Nasarawa

Garkuwa da mutane: 'Yan sanda sun cafke wani basarake a jihar Nasarawa

Hukumar 'yan sandan jihar Nasarawa sun cafke Dalhatu Abubakar, dagacin kauyen Mangora Gina dake karamar hukumar Tunga a jihar Nasarawa. Ana zarginsa da taimakawa tare da tallafawa garkuwa da mutane.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Bola Longe, ya sanar da hakan a ranar Juma'a a garin Lafiya yayin gabatar da dagacin da wasu mutane 80 da ake zargi, ga manema labarai, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Kamar yadda Longe ya ce, jami'an hukumar sun cafke basaraken bayan bayanin sirri mai cike da sahihanci da suka samu a kan hannunsa dumu-dumu cikin garkuwa da mutane da ake yi a yankin Loko a Nasarawa da Toto.

"Mashahurin dan ta'adda ne da aka dade ana labari kuma tuni ya kasance a jerin wadanda muke nema ido rufe," in ji shi.

DUBA WANNAN: Zamfara: Matawalle ya kwace kwangilar N76bn

Ya ce daga ranar 22 ga watan Oktoba zuwa watan Disamba 2019, hukumar ta kama mutane 46 da take zargi da garkuwa da mutane da kuma mutane 35 da take zargi da zama mambobin kungiyar asiri.

'Yan sandan sun bayyana cewa, sun samu bindigogi 9, harsasai 34, adaidaita sahu 3, babura 2 da motoci uku daga wajen wadanda ake zargin.

Kwamishinan ya danganta nasarar hukumar da tallafin da mutane me bada wa. Yayi kira ga jama'a da su cigaba da goyon bayan jami'an tsaro don samun zaman lafiya a jihar.

Ya ja kunnen 'yan ta'adda a jihar da su tuba kafin su shiga hannu ko kuma su bar jihar.

Kamar yadda ya ce, jami'an 'yan sandan jihar a shirye suke don shawo kan matsalolin tsaro a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel