Bidiyon Daloli: Jaafar ya ɓoye kansa sakamakon barazana da ya ke fuskanta
- Jaafar Jaafar, mawallafin jaridar Daily Nigerian da ake wallafawa a intanet ya boye kansa
- Jaafar ya shiga buyan ne saboda abin da ya kira barazana ga rayuwarsa inda ya ce wasu mutane na bin sahunsa duk inda ya tafi
- Hakan na zuwa ne bayan rundunar yan sanda ta gayyaci Jaafar domin amsa tambayoyi kan zargin tada fitina da karya
Mawallafin Jaridar Daily Nigerian, Jaafar Jaafar, wanda ya wallafa bidiyon Gandollar, ya tsere daga gidansa ya shiga buya bayan samun sakonnin barazana da dama.
Hakan na zuwa ne a yayin da ya ke daf da amsa gayyatar yan sanda da ke bincike kan "hadin baki don aikata laifi, bata suna, karya da tada zaune tsaye", Legit ta samu bayani daga bakin wani na kusa da Jafar.
Yace basu son wani IG ke bukatar ganinsa ba, "Idan sabo ne me akayi mishi, in tsoho IG na kuma wani magana ne? shi yasa muka alakanta gayyatar da maganar Ganduje ne"
"Lauyoyin Ja'afar sun bashi shawara kada ya amsa gayyatar, saboda zasu iya rikeshi. sun zo da yan sanda guda uku. wanda ya zo kawo wasikar gayyata, me na kawo yan sanda 3."
KU KARANTA: An yi tonon asiri tsakanin sojoji da wasu fararen hula kan taimakon ƴan Boko Haram
Dan jaridar ya wallafa fayafayen bidiyo na Gwamna Abdullahi Ganduje na Kano a watan Oktoban 2018, yana karbar daloli da ake zargin cewa rashawa ne daga hannun dan kwangila.
A watan Maris, ya rubuta takardar korafi zuwa ga tsohon Sufeta Janar na 'Yan sandan Nigeria, Mohammed Adamu kan barazana ga rayuwarsa.
Hakan na zuwa ne bayan hirar da BBC Hausa ta yi da Ganduje a ranar 19 ga watan Maris inda ya ce zai dauki mataki kan wadanda suka fitar da bidiyon.
KU KARANTA: Hotunan wasu ƴan Nigeria da suka sake karɓar addinin musulunci a Libya
Kafin ya shiga buya, sashin sa ido na IGP na yan sanda ta gayyaci Jaafar domin ya amsa tambayoyi kan zarginsa da tada fitina da yada karerayi.
Ya kamata ya gurfana gaban yan sandan ne a ranar 19 ga watan Afrilu.
A wani labarin daban, dan majalisar tarayya, Sanata Orji Uzor Kalu ya ce ya yi imanin akwai wadanda ke yunkurin yi wa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari zagon kasa.
Dan majalisar mai wakiltan Abia North a majalisar tarayya ya yi wannan furucin ne yayin wata hira da aka yi da shi a Channels TV a ranar Litinin 12 ga watan Afirilu.
Ya ce za a magance kallubalen tsaron inda aka hada kai tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi aka yi aiki tare.
Asali: Legit.ng
Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng
Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164